Tapgun ya ce rigimar cikin-gida za ta yi wa PDP illa sosai a Filato a zabe mai zuwa

Tapgun ya ce rigimar cikin-gida za ta yi wa PDP illa sosai a Filato a zabe mai zuwa

- Fidelis Naanmiap Tapgun ya na tsoron PDP za ta sha kasa a zabe mai zuwa

- Ambasada Fidelis Tapgun ya ce idan aka yi sake, PDP ba za su je ko ina ba

- Tsohon Ministan kasuwancin ya yi kira ga PDP-NWC su duba rikicin Filato

Fidelis Naanmiap Tapgun, ya nuna dar-dar dinsa game da halin da PDP za ta shiga a zaben 2023, ya na ganin jam’iyyar ba za ta yi nasara ba.

Tsohon gwamnan jihar Filato, Fidelis Naanmiap Tapgun Fidelis Naanmiap Tapgun, ya koka a game da rikicin cikin gidan da ke damun PDP.

Ambasada Fidelis Tapgun ya ce matsalar da ta dabaibaye jam’yyar PDP ta reshen jihar Filato, za ta iya zama cikas a babban zabe mai zuwa a 2023.

Fidelis Tapgun wanda ya taba rike kujerar gwamna, minista da jakada a Najeriya ya gargadi ‘yanuwansa a siyasa cewa sai sun tashi tsaye.

KU KARANTA: Ibo ya samu mukami a Gwamnatin Gombe

Jaridar Punch ta rahoto Fidelis Tapgun ya na jan-kunnen PDP cewa sai sun yi da gaske ne za su iya lashe kowace irin kujera a Filato a zaben 2023.

Ambasada Tapgun ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020, an yi wannan tattaunawa ne a Jos.

Tapgun ya yi wannan magana ne yayin da ake jiran zaben cike-gurbi na kujerar Sanatan kudancin Filato, bayan rasuwar Sanata Ignatius Datong Longjan.

Babban ‘dan siyasar ya ce: “A matsayina na wadanda su ka kafa PDP, na damu sosai kan abin da ke damun bangaren jam’iyya na jihar mu.”

KU KARANTA: Kasafin kudin da Buhari ya gabatar ba mai bullewa ba ne – Sanatocin PDP

Tapgun ya ce rigimar cikin-gida za ta yi wa PDP illa sosai a Filato a zabe mai zuwa
Fidelis Tapgun da Chris Hasan Hoto: sunnewsonline.com/pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“Tun farko zaben da ya kawo Chris Hassan da ‘yan majalisarsa, ba zabe ba ne, an kakaba shugabanni ne, domin masu takara sun kaurace wa zaben.”

A karshe, Ambasada ya yi kira ga uwar jam’iyya ta sa baki kan abubuwan da ya ke faruwa a Filato.

A makon nan ne ku ka ji cewa tsohon gwwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya bukaci ya yi sulhu da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom a wajen kotu.

Ana shari’a tsakanin Adams Oshiohmole da Gwamnan Benuwai kan abin da ya faru tun 2018.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel