Zuciya: Matashin dan kasuwa ya saye bankin da ya hanashi rancen kudi shekaru 17 da suka wuce

Zuciya: Matashin dan kasuwa ya saye bankin da ya hanashi rancen kudi shekaru 17 da suka wuce

- Wani ɗan-kasuwa mai suna Adam Deering ya nuna cewa mutum zai iya cimma mafarkan sa ta hanyar juriya da kuma aiki tuƙuru.

- An hana Deering bashin banki na yuro 10,000 (€10,000) lokacin yana da shekaru 22 a duniya, amma daga bisani bayan shekaru 17 ya siye bankin.

- Bankin ya ƙi karɓar buƙatar Deering inda suka ce ya yi ƙaƙanta ga kuma rashin sanayyar kasuwanci

Deering yayi gwagwarmayar rayuwa bayan an hana shi bashin da ya shirya kraba domin ya zuba jari a kasuwanci da ya ke tunanin yi.

An hana Adam Deering bashin yuro 10,000 (£10,000) lokacin yana ɗan shekara 22, amma bayan shekara 17 ɗan-kasuwar, mazaunin garin Manchester, ya siye bankin.

Mahunkuntan bankin sun yanke shawarar hana bashin bayan sun cimma matsayar cewa Deering yana da ƙarancin shekaru da ƙwarewar kasuwanci, kamar yadda rahoton Elite Readers ya bayyana.

Ɗan-kasuwar, wanda ya ke matuƙar buƙatar kuɗi domin ya zuba a kasuwancin da yake tunanin yi, bai bari hana shi bashin ya kashe masa kwarin-guiwarsa ba na ganin mafarkin da yake ya zama gaskiya ba.

DUBA WANNAN: 'Ku daina amfani da fitsari da kashin shanu domin maganin ciwon idanu'

Ɗan-kasuwar mai shekaru 39 yana jan ragamar kasuwanci har guda biyar na mililoyin kuɗaɗe.

Zuciya: Matashin dan kasuwa ya saye bankin da ya hanashi rancen kudi shekaru 17 da suka wuce
Adam Deering da bankin da ya saya
Asali: Instagram

Ya mallaki bankin da adadin kuɗi yuro 450,000 (£450,000) kwatankwacin naira miliyan dubu ɗari biyu da ashirin da huɗu da dubu ɗari takwas da bakwai da ɗari tara da biyar da ɗigo arba'in da huɗu (₦224,807,905.44).

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda

Zama ɗan-kasuwa ba abu ne mai sauƙi ga Deering ba amma hana shi rance ya zamo masa gamo da katari.

Yana tuna cewa: "Ba tare da kuɗin ba na kwashe watanni huɗu ina shan sanyin daɓe a ƙaramin ofishi saboda ba zan iya siyan kujera da teburi ba.

"Watannin kwanan nan suna da wahala, ban san ko zan iya ba ko kuma zan iya biyan abin da ake bina ba"

Deering yana shirin maida bankin wurin siye da siyarwa da kuma wurin zaman mutane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel