Tsohon kakakin majalisar dokokin Jigawa, Illiyasu Dundubus, ya rasu

Tsohon kakakin majalisar dokokin Jigawa, Illiyasu Dundubus, ya rasu

- Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Illiyasu Sa’idu Dundubus, ya mutu

- Dundubus ya amsa kiran mahaliccinsa a yau Laraba, 14 ga watan Oktoba

- Ya rasu ne a garin Zaria, jihar Kaduna inda yake jinya

Allah ya yiwa tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Illiyasu Sa’idu Dundubus, rasuwa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun majalisar dokokin jihar, Babangida Hadejia, ya ce marigayin ya rasu a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, yayinda yake jinya a Zaria, jihar Kaduna.

Mista Hadejia ya ce marigayin ya yi aiki a matsayin kakakin majalisa tsakanin 2000 da 2003 a gwamnatin tsohon gwamna, Saminu Turaki.

KU KARANTA KUMA: Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli

Tsohon kakakin majalisar dokokin Jigawa, Illiyasu Dundubus, ya rasu
Tsohon kakakin majalisar dokokin Jigawa, Illiyasu Dundubus, ya rasu Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Kakakin majalisar dokokin jihar, Idris Garba, ya yi jimamin mutuwar tsohon kakakin wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen dan majalisa, wanda a lokacinsa ya jajirce wajen sama wa bangaren dokoki yanci.

Ya ce ma’aikatan majalisar dokokin sun shiga juyayi da alhini bayan samun labarin mutuwarsa.

Sun kuma mika ta’aziyyarsu ga iyalansa tare da addu’an Allah ya hutasshe shi a jannatul Firdaus.

KU KARANTA KUMA: Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu

A wani labarin kuma, Ƴan Zuru daga jihar Kebbi mazauna jihar Kaduna sun yi addu'a ta musamman ga marigayi Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumban 2020.

Ƴan Zurun sun bayyana marigayi Sarkin a matsayin uba, sun kuma bukaci sabon sarkin, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi koyi da halayen tsohon sarkin musamman na kira ga zaman lafiya.

An ruwaito cewa musulmi har ma da Kirista daga Zuru sun hallarci taron da aka yi a fadar Wakilin Zuru da Kewaye, Injiniya Zubairu Kabiru a unguwar Mahuta da ke Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel