Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli

Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayar da muhimmiyar shawara ga sabon sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

- El-Rufai ya bukaci Bamalli da ya yi adalci ga kowa domin a yanzu an gama takara

- Gwamnan ya jadadda cewa ya janyo kowa a jiki daga wadanda suka yi masa mubaya’a har wadanda basu yi masa ba

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, da ya zama adali ga dukkanin al’umman masarautar.

Gwamnan ya fada ma sarkin cewa gasar neman kujerar ya kare don haka akwai bukatar sarkin ya hada kan mutane, harda wadanda basu goya masa baya ba.

Gwamna El-Rufai ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar sarkin a gidan gwamnati yayinda suka kai masa ziyarar godiya a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Saurayi ya nemi auren budurwa a taron zanga zangar EndSARS, ta amince

Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli
Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

“Rokona shine ka ci gaba da hada kan kowa da kowa, ka ja kowa a jiki, ka koyi darusa daga gogewar mambobin majalisar masarautar Zazzau.

“Domin aiki tare zai kai masarautar Zazzau ga tubalin nasara da ci gaba, zai kawo zaman lafiya da hadin kai. Ina kira ga sarkin da ya zama adali ga kowa. Ga wadanda suka yi masa mubaya’a da wadanda basu yi masa ba saboda gasa ya kare.

"Babban aikin yanzu shine fara hada kan kowa da kowa, cimma nasara da kare martabar wannan masarauta da dukkanmu muke alfahari da ita,” in ji shi.

Da farko, Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya fada ma gwamnan cewa sun zo gidan gwamnati domin mika godiya a kan zabarsa da ya yi a matsayin magajin marigayi sarki Dr Shehu Idris.

Ya ce ba karamin aiki bane saboda gasar da aka fuskanta a lokacin zaben amma ya ba gwamnan tabbacin samun biyayyan masarautar.

KU KARANTA KUMA: Mutanen Zuru mazauna Kaduna sun yi wa marigayi Shehu Idris addu'a ta musamman

Ya kuma fada ma gwamnan cewa akwai wakilan dukkanin daular a tawagarsa wanda hakan ke nufin akwai hadin kai da zaman lafiya a masarautar.

“Saboda haka na yarda cewa mu ahli guda ne kuma bana ganin akwai wani dalili da zai sa a ware kowani daula. Dukkanmu yan uwa ne kuma mun dade a tare. Na rike mukamin Magajin Gari na tsawon shekaru 19 don haka ina da kwarewar da zan yi aiki da kowa,” in ji shi.

An nada sarki Bamalli a matsayin sarkin zazzau na 19, a ranar 7 ga watan Oktoban 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel