Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa

Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa

- Ambaliyar ruwa na cigaba da faruwa a jihar Jigawa a inda tayi sanadiyyar mutuwar yara 4 a karamar hukumar Gwaram

- Kakakin 'yan sanda na jihar, Abdu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin tattaunawa da gidan talabijin din Channels

- Inda yace yaran 4 na hanyar su ta komawa gida daga gona sai suka zo tsallake rafi, wanda hakan ya zama ajalinsu

Ruwa ya tafi da yara 4 a lokacin da suke kokarin tsallake rafi daga gonarsu da take Kafin Doki a garin Sara dake karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Jam'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Abdu Jinjiri ya tabbatar wa gidan talabijin din Channels faruwar al'amarin, inda yace yanzu haka an tsinci gawawwaki 3, 1 kuma ba'a ganta ba har yanzu.

A cewarsa, "Ruwa ya tafi da Bilkisu Haruna mai shekaru 17, Shamsiyya Nuhu mai shekaru 13, Maryam Danlami mai shekaru 12 da Marakisiyya Musa a lokacin da suke kokarin komawa gida daga gona.

"Yanzu haka mun ga gawawwaki 3 daga ciki amma har yanzu bamuga Marakisiyya ba," a cewarsa.

A 'yan kwanakin nan jihar Jigawa na fuskantar ambaliyar ruwa wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 41, kuma yayi sanadiyyar rasa muhallin iyalai 1000.

KU KARANTA: EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa
Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa. Hoto daga ChannelsTV
Asali: UGC

KU KARANTA: Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da sabuwar rundunar SWAT ta 'yan sanda

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, SAN, na samar da ayyuka na musamman daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamban shekarar 2020.

Tsarin zai kunshi samarwa mutane 1000 ayyukan watanni 3 daga kowacce karamar hukuma 774 dake kasar nan.

A takardar da ministan yasa hannu jiya Litinin, yace shugaban kasar ya amince da bukatar ta shi ne idan ruwa ya dauke, sai dai har yanzu ruwan bai dauke ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: