Ta’addanci: Yan gudun hijira na iya komawa Baga domin akwai tsaro yanzu, gwamnatin Borno
- An kaddamar da cewar yan gudun hijira na iya komawa garin Baga da ke Borno
- Kwamishinan shari’a a jihar, Kaka-Shehu Lawan ne ya bayyana hakan
- Lawan a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro na ba garin kariya
Ana shirye-shiryen mayar da yan gudun hijira da ke Borno zuwa garin Baga, daya daga cikin wuraren da yan ta’addan Boko Haram suka kaddamar da hare-hare a baya-bayan nan.
Atoni janar kuma kwamishinan shari’a a jihar, Kaka-Shehu Lawan, a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya yi bayani kan dalilin da yasa gwamnati ta yanke wannan shawarar.
KU KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga
Lawan, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, ya yi ikirarin cewa garin Baga na da cikakken tsaro a yanzu da yan gudun hijira za su iya komawa.
Hakan ya biyo bayan hare-hare biyu da aka kai wa motocin Gwamna Babagana Zulum a garin.

Asali: Twitter
Kwamishinan wanda ke jagorantar kwamitin da ke kula da ragamar mayar da yan gudun hijiran, ya ce lallai hare-haren da aka kai wa gwamnan bai da nasaba da yanayin tsaron garin gaba daya.
KU KARANTA KUMA: EndSARS: Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock
Harma Lawan ya ce shi da tawagarsa sun shafe tsawon kwanaki hudu a garin Baga a lokacin sake bude garin kuma basu fuskanci wani lamari na tashin hankali ba.
Ya jadadda cewa a yanzu garin cike yake da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin bayar da kariya.
Ya ce:
“Kwamitinmu ya shafe kwanaki hudu a garin kuma ina iya tabbatar maku da cewa akwai tsaro sosai a Baga kuma akwai tarin sojoji a wajen.
“A kwanaki hudu da muka kwashe a Baga, bamu samu wani barazana na tsaro ba. Mun fita mun yi yawo a garin don duba ayyukan da ya kamata ayi ba tare da fargaba ba.
"Bayan aikin rangadin mu kan koma masaukinmu da ke cikin garin mun kwana. Ba a samu lamari na harbi ba ko sau daya.
“Hatta lokacin da gwamnan ya zo, ya kwana a Baga kuma ba a samu tashin hankali ba.”
A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya bukaci hukumar yan sanda da ta tura jami’an rundunar SARS da aka rushe zuwa jihar domin bayar da gudunmawa a yaki da yan ta’addan Boko Haram.
An dai soke sashin rundunar ta yan sanda sannan aka rarraba jami’ata zuwa wasu bangarorin biyo bayan zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng