Gwamnan Ribas ya shiga cikin masu zanga-zanga bayan ya haramta #EndSARS

Gwamnan Ribas ya shiga cikin masu zanga-zanga bayan ya haramta #EndSARS

- Nyesom Wike ya shiga cikin masu zanga-zangar #EndSARS a Fatakwal

- Gwamnan ya lashe aman da ya yi na cewa ba zai bari ayi zanga-zanga ba

- Wike ya ce dama tun farko ya na cikin wadanda su ke adawa da F-SARS

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya lashe amansa na haramta zanga-zangar da ake yin a #EndSARS.

Mai girma Nyesom Wike ya shiga cikin sahun masu wannan zanga-zanga, har kuma ya yi kira da a yi wa hukumar ‘yan sandan Najeriya garambawul.

Gwamnan ya yi wannan ne bayan kwana guda da fitar da jawabi inda ya ce ba zai yarda da zanga-zanga a jiharsa ba, ganin cewa IGP ya rusa SARS.

KU KARANTA: An sallami SARS, an kafa SWAT

Da ya ke jawabi a gaban masu zanga-zangar, Wike ya ce ko da ya ke ba goyon bayan abin da jama’an su ke yi, ya na cikin masu sukar aikin ‘yan sanda.

Gwamna Wike ya ce babu gwamnan da ya kalubalanci jami’ar tsaro kamar yadda ya yi a baya.

“Ba na goyon bayan mu zo nan. Na rantse zan kare lafiya da dukiyoyin mutanen jihar Ribas. Jinanan jihar Ribas ya na da daraja a wurina.” inji gwamnan.

Ya ce: “Ribas ta sha wahala a hannun SARS. Lokacin da mu ka fallasa danyen aikin da SARS su ke yi, ba a kulamu ba, yanzu aikinsu ya bulla a wasu wurare.”

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya gana da Buhari a kan #EndSARS

Gwamnan Ribas ya shiga cikin masu zanga-zanga bayan ya haramta #EndSARS
Nyesom Wike Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Babu gwamna a kasar nan da ya kalubalanci SARS kamar yadda mu ka yi. Lokacin da ake yawon garkuwa da mutane, na kai kuka wajen gwamnatin tarayya.”

Wike ya ce shi kadai ne gwamnan da ya fita zanga-zangar a doke SARS. “Mun rasa mutane rututu saboda SARS a nan. Babu jihar da ta mara mana baya.”

A jiya kun ji cewa Nyesom Wike ya soki yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kara albashin Malaman makaranta a ranar malamai ta Duniya.

Wike ya ce ya kamata a tuntubi duk sauran gwamnonin jihohi kafin a dauki wannan mataki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel