Oshiomhole ya bukaci ayi sulhu da Gwamnan Benuwai Ortom a wajen kotu inji Lauya

Oshiomhole ya bukaci ayi sulhu da Gwamnan Benuwai Ortom a wajen kotu inji Lauya

- Ana shari’a tsakanin Adams Oshiohmole da Gwamnan Benuwai Samuel Ortom

- A 2018 Adams Oshiohmole ya zargi Gwamnan da hannu a kisan wasu Malamai

- Wannan ya sa Ortom ya shiga kotu da tsohon gwamnan, ye ce ya yi masa kazafi

Tsohon shugaban kasan jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bukaci ayi ta ta kare tsakaninsa da gwamna Samuel Ortom ba tare da an kai ga kotu ba.

Kwanaki gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom ya maka Adams Oshiomole a kotu, ya bukaci ya biya sa Naira biliyan 10 bisa zargin yi masa karya.

Idan za ku tuna a watan Yulin 2018 ne Adams Oshiomole ya kira taron manema labarai, inda ya zargi Samuel Ortom da hannu a kisan wasu fastoci biyu.

KU KARANTA: Hadimin Shugaban kasa ya karyata rade-radin kai karar Dawisu gaban Buhari

A dalilin wannan ne gwamnan ya kai kara gaban kotu, kafin a kai ko ina, Alkali ya yi fatali da wasu hujjoji da Oshiomhole ya bada domin ya kare kansa.

An koma gaban kuliya a ranar Talatar nan, Lauyan da ya tsayawa gwamnan, Samuel Irabor, ya bayyanawa kotu cewa sun shirya gabatar da shaidunsu.

Shi kuma Festus Jumbo, wanda ya ke kare tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ya sanar da kotu cewa babu dalilin yin haka, za su janye maganarsu.

Jumbo ya fadawa Alkali su na tunanin lashe amansu, kuma za su fitar da jawabi a mako guda.

KU KARANTA: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun hadu da Janar Ibrahim Babangida

Oshiomhole ya bukaci ayi sulhu da Gwamnan Benuwai Ortom a wajen kotu inji Lauya
Gwamnan Benuwai Ortom Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Mai kare tsohon shugaban jam’iyyar APC ya fadawa Alkali Augustine Ityonyiman na babban kotu da ke garin Makurdi za su ranar da za su nemi ayi sulhu.

Mai shari’a Ityonyiman ya daga shari’ar zuwa 29 ga watan Oktoba domin bangarorin su sasanta.

A jihar Kano kuma kun ji cewa za ayi zaben kananan hukumomi. Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi kafin su iya tsayawa takara.

Gwamnati ta ce duk wanda aka samu ya na shan miyagun kwayoyi, zai tafi cibiyar sauya halaye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel