Zulum ya goyi bayan SARS, yana so a dawo da jami’an rundunar jiharsa

Zulum ya goyi bayan SARS, yana so a dawo da jami’an rundunar jiharsa

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana matsayarsa kan rundunar SARS

- Zulum ya ce yana goyon bayan rundunar dari-bisa-dari

- Ya bukaci hukumar yan sanda ta dawo da rundunar wacce aka rushe jiharsa domin su yi yaki da ta'addanci

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya bukaci hukumar yan sanda da ta tura jami’an rundunar SARS da aka rushe zuwa jihar domin bayar da gudunmawa a yaki da yan ta’addan Boko Haram.

An dai soke sashin rundunar ta yan sanda sannan aka rarraba jami’anta zuwa wasu bangarorin biyo bayan zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar a kasar.

Kasa da kwanaki biyu bayan soke rundunar yan sandan, an sake gudanar da gagarumin zanga-zanga kan ayyukanta a ranar Talata a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga

Zulum ya yi kiran ne a lokacin da wata tawaga karkashin jagorancin ministan cikin gida, Rauf Argebesola suka gana da shi a gidan gwamnati, Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Zulum ya goyi bayan SARS, yana so a dawo da jami’an rundunar jiharsa
Zulum ya goyi bayan SARS, yana so a dawo da jami’an rundunar jiharsa Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce jami’an rundunar da aka soke sun taka muhimmiyar rawar gani a ayyukan yaki da ta’addanci da karfinsu musamman a yaki da Boko Haram.

Ya ce: “Ba ma goyon bayan cin zarafi daga kowani jami’in tsaro, amma maganar gaskiya, a nan jihar Borno bai kamata a wofantar da kokarin jami’an SARS ba a yaki da suke da ta’addanci.

“Suna kokari matuka wajen magance matsalar tsaro a jihar Borno. Sun taimakawa kokarin rundunar sojin Najeriya sosai,” in ji Zulum.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock

A baya mun ji cewa wasu kungiyoyin jama’a da na yan kasuwa a jihar Borno sun fito unguwa don yi zanga-zangar rashin jin dadi ruguza rundunar yan sandan SARS da gwamnatin Tarayya ta yi.

Masu zanga-zangar na so rundunar SARS ta ci gaba da ayyukanta a jihar Borno.

Shugaban gamayyar kungiyar a Borno, Ahmed Shehu, ya ce koda dai basa farin ciki da Abunda ke gudana a wasu sassan kasar, “jami’an SARS sun taimaka sosai wajen yaki da ta’addanci.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel