Abin da na tattauna da shugaba Buhari a kan zanga-zangar EDNSARS - Gwamnan Legas

Abin da na tattauna da shugaba Buhari a kan zanga-zangar EDNSARS - Gwamnan Legas

- Gwmnan jihar Legas, Babajie Sanwo-Olu, ya bayyana abubuwan da ya tattauna da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayin ganawarsu

- Kafin ganawarsa da shugaba Buhari ya gana da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu

- Ganawar Sanwo-Olu da Buhari da IGP na da alaka da zanga-zangar da matasa ke yi ta neman a rushe rundunar SARS

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan zanga-zangar da matasa ke yi a fadin kasa domin nuna kyama a kan zaluncin wasu jami'an 'yan sanda.

Yayin tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da Buhari, Sanwo-Olu, ya bayyana abin da ya kai shi fadar shugaban kasa.

A cewar Sanwo-Olu, ya ziyarci Buhari domin tattauna batun zanga-zangar da matasa ke yi a kan a soke rundunar SARS da hana zaluntar jama'a da wasu jami'an 'yan sanda ke yi.

Kazalika, ya bayyana cewa ya sanar da shugaba Buhari irin rawar da gwamnoni ke takawa wajen ganin zanga-zangar ta lafa.

"Na samu damar ganawa da shugaban kasa a gurguje. Ya karramani ta hanyar bani lokaci duk da kasancewar a lokacin ya kammala wani muhimmin taro da sauran gwamnoni.

"Makasudin ganawar shine domin na isar da sakon matasa daga sassan Najeriya a kan neman a kawo karshen rundunar SARS zuwa gareshi.

KARANTA: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 15 a jihar Borno

Abin da na tattauna da shugaba Buhari a kan zanga-zangar EDNSARS - Gwamnan Legas
Buhari da Sanwo-Olu
Asali: Twitter

"Shugaba Buhari ya karbi takardar wasikar da matasan su ka bani cikin girmamawa har ma mun karanta abinda ta kunsa a takaice. Na kuma yi ma sa bayani a kan dukkan abubuwan da mu ke yi a kan zanga-zangar," a cewar Sanwo-Olu.

A cewar Sanwo-Olu, kafin ganawarsa da Buhari, ya gana da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, a kan batun zanga-zangar.

KARANTA: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa

Da yammacin ranar Talata ne IGP Adamu ya sanar da kafa sabon sashe mai lakabin 'SWAT' wanda zai maye gurbin sashen SARS da aka rushe.

Sai dai, tun kafin sashen ya fara aiki, matasan da ke zanga-zanga sun ce an raina mu su wayo ne kurum, domin an sauyawa SARS suna ne kawai bayan sanar da cewa an rusheta.

Matasan sun fara nuna alamun cewa za su fara sabon gangami da tattakin nuna kin yarda da kirkirar SWAT.

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya ce bi umurnin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, na ruguza sashen rundunar SARS.

Odumosu, wanda ya gana da wasu lauyoyi da suke zanga zanga kan cin zarafin da jami'an SARS ke yiwa jama'a, ya ce tuni aka kwace makamai daga hannun jami'an rundunar SARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel