2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

- An bayyana wasu yan takara 10 daga yankin kudu maso gabas wadanda ake so su karbi shugabanci a 2023

- Yan takarar sun hada da tsoffin gwamnoni, ministoci, da manyan masana a fannin tattalin arziki da kuma masu rike da mukamin siyasa a yanzu

- Wata kungiya, COSEYL, wacce ta jero sunayen ta jadadda cewa Shugabancin Igbo a 2023 babu gudu ba ja da baya

Yayin tattaunawa kan wanda zai karbi ragamar shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 ke kara tsananta, wata kungiyar Igbo ta jero sunayen mutane goma wanda ka iya fafatawa don shugabantar kasar a 2023.

Kungiyar, Coalition of South East Youth Leaders (COSEYL), ta bayyana hukuncin da ta yanke bayan babban tarota na kasa a Owerri, babbar birnin jihar Imo.

Da suke magana a madadin sauran mambobin kungiyar, shugaban na COSEYL, Goodluck Ibem da sakatare, Kanice Igwe sun ce shugabancin Igbo babu gudu babu ja da baya a 2023.

Shugabannin kungiyar sun ce sun kafa wani kwamiti mai suna Igbo Presidential Actualization Committee (IPAC) wanda ya fito da sunayen wasu manyan yayan yankin da ka iya neman shugabanci bayan mulkin Buhari.

2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas
2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas Hoto: @dailysunsa
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye)

Daga cikin wadanda ta bayyana a matsayin yan takara da suka cancanta akwai Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, masaniyar tattalin arziki, Ngozi Okonjo-Iweala.

Sai tsoho gwamnan jihar Anambra kuma bulaliyar majalisa a yanzu, Orji Uzor Kalu.

Sauran sune jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Farfesa Kingsley Moghalu.

Tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu sun samu shiga sunayen.

KU KARANTA KUMA: Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni

Sai tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, tsohon ministan sufuri, Kema Chikwe, Cif Onwuasoanya, da kuma Eboe-Osuji wanda ya kasance alkali a kotun kasar waje a Hague.

A wani labarin, Sanatocin jam'iyyar hamayya a majalisar dattawa sun yi Alla-wadai da nadin Lauretta Onochie matsayin kwamishana a hukumar INEC da shugaba Buhari yayi.

Martani kan hakan, shugaban marasa rinjaye a majalisa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce nadin Lauretta ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel