'Yan Boko Haram sun yanka manoma 15 a jihar Borno

'Yan Boko Haram sun yanka manoma 15 a jihar Borno

- Har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram da takwarorinsu na kungiyar ISWAP na cigaba da kai hare-hare a kan fararen hula

- Mayakan na kashe farar hula ne bisa zarginsu da bawa rundunar soji da sauran jami'an tsaro bayanai

- Fararen hula da ke taimakawa wajen yaki da 'yan Boko Haram (CJTF) sun sanar da cewa 'yan Boko Haram sun yanka manoma a kauyen Ngwom

A ranar Talata ne fararen hula da ke taimakawa wajen yaki da 'yan Boko Haram (Civilian JTF) su ka sanar da cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wa manoma 15 yankan rago, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na APF cewa 'yan Boko Haram sun kama manoma 15 yayin da su ke aiki a gonakinsu a kauyen Ngwom, mai nisan kilomita 14 a gabashin Maiduguri.

Sun bayyana cewa 'yan ta'addar sun yi wa manoman yankan rago kuma 14 daga cikinsu sun rasu.

KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa

"Sun yi wa manoman yankan rago, 14 daga cikinsu sun mutu, daya kuma ya rayu da mummunan yanka a wuyansa," a cewar Babakura Kilo, shugaban Civilian JTF.

'Yan Boko Haram sun yanka manoma 14 a jihar Borno
Zulum yayin bawa bazawara tallafin N20m bayan kisan mijinta; Kanal D. C Bako
Asali: Twitter

Ibrahim Liman, mamba a Civilian JTF, ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun dira gonakin kauyen yayin da manoman ke aiki a gonakinsu da tsakar rana. Ya ce manoma 14 sun mutu nan take.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda ma su zanga-zanga su ka kwaci dan sanda a hannun 'yan daba

"An garzaya da wanda ya rayu zuwa asibiti duk da ya na cikin mawuyacin hali," a cewar Liman.

Kungiyar Boko Haram da babbar kawarta, kungiyar ISWAP, na cigaba da kai hare-hare a kan makiyaya, manoma, masunta da sauran fararen hula a sassan jihar Borno.

Mayakan na zargin cewa manoma da sauran fararren hula mazauna kauyuka na bayar da muhimman bayanai a kansu ga rundunar soji.

A wani labarin, IGP, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami'an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an idan sun je Abuja, za ayi masu gwajin kwakwalwa a shirye shiryen yi masu horo don rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel