Yanzu-yanzu: Yan sanda akalla 2 sun mutu, 10 sun jiggata a mumunan hadarin mota (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Yan sanda akalla 2 sun mutu, 10 sun jiggata a mumunan hadarin mota (Hotuna)

- Motar yan sanda tayi mumunan hadari a jihar Ondo ranar Talata

- Kakakin hukumar yan sanda ya bayyana cewa an garzaya da wadanda ta ritsa da su asibiti

- Wannan shine karo na biyu da za'a yi rashin yan sanda sakamakon hadarin mota a shekarar nan

Akalla jami'an yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayinda 10 suka jiggata a mumuman hadarin motan da ya auku a titin Oba Ile, a Akure, birnin jihar Ondo ranar Talata, Channels ta ruwaito.

An tattaro cewa yan sandan dake cikin mota kirar Toyota Hilux sun nufi hanyar tashar jirgin sama yayinda hadarin ya faru.

Wani mai idon shaida ya ce hadarin ya faru ne sanadiyar gudun da yan sanda keyi.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da aukuwan haka amma bai san adadin wadanda suka mutu ba.

"Sai na je asibitin da aka kaisu domin sanin adadin wadanda abin ya shafa." Yace

Ya kara da cewa tayar motar ce ta fashe kuma tayi kudumbala.

DUBA WANNAN: Buhari ya zabi hadimarsa matsayin kwamishana a hukumar INEC

Yanzu-yanzu: Yan sanda akalla 5 sun mutu a mumunan hadarin mota (Hotuna)
Credit: http:/saharareporters.com/news
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Watanni uku da suka wuce, mun kawo muku cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a mumunan hadarin mota da ya auku ga jami'an sanda da aka yiwa horo na musamman watau 'special forces' a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ba'a san abinda ya sabbaba hadarin ba. Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa hadarin ya auku misalin karfe 4:30 na la'asar, kusa da barikin Sojin Jaji, inda mota dauke yan sanda tayi kuli-kulin kubura.

Wani direban motar haya 'Sharon' da ya shaida hadarin, Hassan, ya bayyana cewa: "Mumunan hadari ne saboda na kirga kimanin gawawwakin yan sanda bakwai a tsakiyar titi."

"Wasu biyu sun yi mugun jikkata yayinda sauran suna tsira."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel