Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye)

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye)

- Majalisar dattawa ta tabbatar da wasu nade-nade da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike mata

- An tabbatar da nadin manyan alkalan kotun daukaka kara su takwas inda suka koma alkalan kotun koli

- Hakan ya biyo bayan shawarar kwamitin majalisar dattawa kan shari’a wacce ta tantance su

Majalisar dattawa a ranar Talata ta amince tare da tabbatar da nadin alkalan kotun koli su takwas.

Shugaban kasa Muhammdu Buhari ta wasika da ya aike zauren majalisa wanda shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta, ya bukaci majalisar da ta amince da nadin alkalan guda takwas.

Buhari ya bayyana cewa nadin ya kasance bisa shawarar majalisar alkalai ta kasa.

KU KARANTA KUMA: Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye)
Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye) Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Buhari ya kuma bayyana cewa matakin nasa ya kasance “daidai da sashi 231(2) na kundin tsarin 1999 kamar yadda aka gyara kuma bisa shawarar majalisar alkalai ta kasa daidai da matsayinsu da kuma girmansu a kotun daukaka kara.”

Wadanda aka nada sune, Lawan Garba (Arewa ta Yamma), Helen Ogunwumiju (Kudu ta Yamma), Abdu Aboki (Arewa ta Yamma), da kuma M M Saulawa (Arewa ta Yamma).

Sauran sune, Adamu Jauro (Arewa ta Gabas), Samuel Oseji (Kudu ta Kudu), Tijani Abubakar (Arewa ta Gabas), da kuma Emmanuel Agim (Kudu ta Kudu).

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan shari’a, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da rahoton kwamitinsa na tantancewar don sanatoci su duba a ranar Talata.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hadimarsa ta Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, a matsayin daya daga cikin kwamishanonin hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC.

Buhari ya gabatar da sunanta da wasu mutane uku gaban majalisar dattawa domin tantancesu da tabbatar da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel