Sabon tsarin albashin Malamai zai jawo matsala inji Gwamna Nyesom Wike

Sabon tsarin albashin Malamai zai jawo matsala inji Gwamna Nyesom Wike

- Nyesom Wike ya soki yadda gwamnatin tarayya ta kara albashin Malamai

- Gwamnan ya ce ya kamata a tuntubi jihohi kafin a dauki wannan matakin

- Wike ya ce Jihohi su na jiran a sake duban yadda ake rabon arzikin Najeiya

A ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, 2020, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi magana game da karin albashin da aka yi wa malamai a Najeriya.

Nyesom Wike ya na ganin cewa kara wa malamai albashi zai iya jawowa harkar ilmi matsala.

Gwamna Nyesom Wike ya bayyana haka ne lokacin da wakilan shugabannin sashen koyon aikin likita na jami’ar jihar Ribas su ka kai masa ziyara a Fatakwal.

KU KARANTA: Za a kashe N270m wajen sayen tayoyin mota da abincin Shugaban kasa

Ma’aikatan sun gana da gwamnan Ribas a gidan gwamnati kamar yadda Punch ta fitar da rahoto.

Bayan ganawar ne gwamnan ya fitar da jawabi ta bakin kwamishinarsa ta yada labarai, Paulinus Nsirim, ya na sukar yadda gwamnati ta yi wannan kari.

Paulinus Nsirim ta rahoto gwamnan ya na cewa abu ne mai kyau karin da aka yi, sai dai ya na ganin babu dalilin a siyasantar da irin wannan lamari na ilmi.

“Abu ne mai kyau a kula da malamai saboda muhimmin amfaninsu a cikin al’umma, amma dole a bi a hankali wajen dabbaka wannan mataki.” Inji Gwamnan.

KU KARANTA: An ware N10.5bn domin ayi wa fadar Shugaban kasa faci a kasafin 2021

Sabon tsarin albashin Malamai zai jawo matsala inji Gwamna Nyesom Wike
Shugaba kasa tare Gwamna Nyesom Wike Hoto: Hutudole
Asali: UGC

Ya ce: “Gwamnatin tarayya ba ta duba maganar sake duban yadda ake rabon kudin kasa ba, amma ta na sake kinkimo wa kanta aiki ba tare da ta tuntubemu ba.”

Dole abin da gwamnatin tarayya ta ke kashewa ya karu idan har aka tabbatar da wannan kari da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa malamai kwanan nan.

Da ya ke jawabi, gwamna Wike ya yi alkawarin cewa sai sashen koyon aikin likita na jami’ar jihar Ribas ya zama cikin wadanda su ka fi kowane a fadin Najeriya.

Kwanakin baya kun ji cewa gwamnatin Ribas ta yi barazanar shiga kotu da gwamnatin tarayya a kan cire kudi daga asusun hadaka ba tare da tuntubar jihohi ba.

Gwamna Nyesom Wike ya ce zai kalubalanci kudin da Buhari ya sa aka zara daga FAAC

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng