Yanzu Yanzu: Zanga-zangar neman a dawo da rundunar SARS na gudana a Borno

Yanzu Yanzu: Zanga-zangar neman a dawo da rundunar SARS na gudana a Borno

- A yanzu haka ana nan ana gudanar da zanga-zangar lumana na neman a dawo da rundunar SARS a garin Maiduguri

- Kungiyoyin jama'a da na yan kasuwa a Borno sun jadadda cewa rundunar ta SARS na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta'addanci

- Sun bukaci a dawo da SARS jihar ta Borno domin zaman lafiyarsu

Wasu kungiyoyin jama’a da na yan kasuwa a jihar Borno sun fito unguwa don yi zanga-zangar rashin jin dadi ruguza rundunar yan sandan SARS da gwamnatin Tarayya ta yi.

Masu zanga-zangar na so rundunar SARS ta ci gaba da ayyukanta a jihar Borno.

Shugaban gamayyar kungiyar a Borno, Ahmed Shehu, ya ce koda dai basa farin ciki da Abunda ke gudana a wasu sassan kasar, “jami’an SARS sun taimaka sosai wajen yaki da ta’addanci.”

Yanzu Yanzu: Zanga-zangar neman a dawo da rundunar SARS na gudana a Borno
Yanzu Yanzu: Zanga-zangar neman a dawo da rundunar SARS na gudana a Borno Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya ziyarci Babangida a gidansa

Masu zanga-zangar wadanda suka dauki kwalayen sanarwa sun ce “Mu na son SARS don zaman lafiya a Borno.”

A yanzu haka suna nan suna tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar Borno a Maiduguri, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARATA KUMA: SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

A gefe guda, Sanata Kabiru Garba Marafa ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bude idanunsa da kyau, cewa zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar a fadin kasar ya kasance makarkashiya da aka yi kan gwamnatinsa.

Marafa wanda ya kasance dan gaba-gaba a takarar gwamna na APC a jihar Zamfara a zaben 2019, ya ce sharrin ruguza rundunar SARS ya fi alkhairinsa yawa.

“Akwai bukatar shugaban kasa ya bude idanunsa sannan ya yi taka-tsan-tsan sosai. Shugaban kasar na iya fadawa tarkon makiyansa. Matsayana shine cewa wasu mutane sun matsu su ga sun tunkude wannan gwamnati ta kowani hali.

"Da wannan zanga-zanga da aka gudanar don kira ga soke rundunar SARS, ina fargaba muna iya shiga cikin manyan matsaloli, musamman daga inda na fito. Daga karshe, wadannan mutanen za su fito su zargi gwamnati da gaza kare kayukar yan kasa,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel