Fadar Shugaban kasa ta ware miliyoyi domin girki da liyafa a shekara mai zuwa

Fadar Shugaban kasa ta ware miliyoyi domin girki da liyafa a shekara mai zuwa

- Fadar Shugaban kasa ta yi kasafin miliyoyi a matsayin kudin abinci

- A shekarar badi, za a canza tayoyin motocin Aso Villa a kan N116m

- Wadannan su na cikin kasafin kudin da ake jira majalisa ta tabbatar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, za su kashe N167, 459, 107 wajen cin abinci da kayan dadi a shekarar badi.

Idan har kasafin kudin shekara mai zuwa ya samu karbuwa a majalisar tarayya, fadar shugaban kasar za ta batar da wadannan makudan kudi a girki.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa shugaban kasa ya ware N98, 306, 492 domin sayen abinci da kayan girki a cikin kasafin kudin na shekara mai zuwa.

KU KARANTA: An ware N10.5bn domin ayi wa fadar Shugaban kasa faci a kasafin 2021

Haka zalika mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya na shirin kashe N50, 888, 218 kan abinci, ma’ana kusan dai rabin da aka ware wa shugaba Buhari.

Rahoton da jaridar ta fitar a ranar 13 ga watan Oktoba, 2020, ya nuna cewa fadar shugaban kasa za ta batar da kusan Naira miliyan 150 a abinci a badi.

Bayan haka an ware wasu N18, 264, 397 domin liyafa a fadar shugaban kasar. Za a fitar da wannan kudi ne daga wasu Naira miliyan 82 da aka kasafta.

Fadar shugaban kasa ta ware wasu Naira miliyan 82.79 a ofishin mataimakin shugaban kasa saboda larurori da bukata da za su iya fadawa kwatsam a 2021.

Fadar Shugaban kasa ta ware miliyoyi domin girki da liyafa a shekara mai zuwa
Shugaban kasa a gaban Majalisa Hoto: Twitter/Bashir Ahmaad
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babu kudin tallafin mai a kasafin shekarar 2021 - Buhari

Rahoton bai tsaya nan ba kurum, an fahimci cewa ana sa ran a kashe Naira miliyan 116 wajen sayen tayoyi na motocin da ke cikin fadar shugaban kasa.

Wadannan motoci kirar ‘Saloon’ da ‘Jeep da gingimari da motocin aiki, da ake amfani da su a fadar ba su jin harbin bindiga, harsashi ba zai iya ratsa su ba.

Ku na da labari cewa Atiku Abubakar ya soki yadda aka tsara kasafin kudin shekarar 2021. Atiku ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sake lissafi.

Atiku ya ce bashin da ake shirin karbowa a badi, ya zarce 3% na GDP, hakan ya saba doka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel