Zaben WTO: Ka taimaka ka yi min kamfen a wurin shugabannin duniya - NOI ta roki Buhari

Zaben WTO: Ka taimaka ka yi min kamfen a wurin shugabannin duniya - NOI ta roki Buhari

- Tsohuwar ministr kudi a lokacin mulkin jam'iyyar PDP, Ngozi Okonjo-Iweala ta ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadarsa

- Ngozi ta samu nasara a zagayen farko na zaben kujerar shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO)

- Buhari ya bawa tsohuwar ministar tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da dukkan karfi da ikonta don ganin ta samu nasara a zagayen karshe na zaben

Shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya tabbatarwa da Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar kuɗi, cewa gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwuwa don ganin ta zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya(WTO).

Buhari ya yi alƙawarin ne yayin da Okonjo-Iweala ta kai masa ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Okonjo-Iweala da Yoo Myung-hee (ministar kasuwanci ta ƙasar koriya ta kudu), sune ƴan takara da suka kai matakin ƙarshe na neman kujerar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

Duk wadda ta samu nasarar lashe zaben kujerar a tsakaninsu itace za ta kasance mace ta farko da ta taɓa shugabantar ƙungiyar kasuwanci ta duniya tun daga kafa ƙungiyar shekaru ashirin da biyar da suka gabata.

KARANTA: Kasafin kudi: Buhari da Osinbajo sun ware N3.2bn domin tafiye-tafiye zuwa ketare a 2021

Acewar Buhari,Okonjo-Iweala ita tafi cancanta da samun matsayin idan aka yi duba ga irin ƙwazo da kuma himma da ta ke da shi a gudanar da aikinta a ƙasa dama duniya baki ɗaya.

"Ina mai tabbatar da cewa za muyi duk yadda zamu iya don ganin kin zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

"Ba wai kawai don ke ƴar Najeriya ba ce, saboda ke ƴar ƙasa ce mai ƙwazo da kuma aiki tuƙuru. Kin cancanci hakan."Acewar Buhari.

Buhari ya daɗa tabbatar mata da cewa zai tuntuɓi wasu shugabannin duniya ta hanyar kiran waya da kuma wasiƙa don neman goyon bayansu.

"Na yi irin hakan ga Dr Akinwunmi Adesina da ya nemi Shugaban Bankin cigaban Afirka (AfDB).

Dukkaninku kun yiwa kasa aiki a ƙarƙashin jam'yyar PDP. Gabaɗayanku kun cancanta matuƙa," a cewarsa.

Zaben WTO: Ka taimaka ka yi min kamfen a wurin shugabannin duniya - NOI ta roki Buhari
Buhari da Ngozi
Asali: Twitter

"Zamu ci gaba da baku goyon baya. Zan yi kiran da hanzari."

Yayin da ta ke magana a kan goyon bayan shugaban ƙasar, Ngozi ta ce tana alfahirin zama ƴar Najeriya.

Ta kuma jinjinawa shugabannin ƙungiyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka a bisa nuna kulawarsu.

KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar har gida

Ta roƙi Buhari da ya yi yunƙuri na ƙarshe cikin satin nan don ganin Koriya ta sha kaye sannan Najeriya ta samu nasara ta hanyar tuntuɓar manyan shugabannin duniya.

Ta kuma godewa sauran waɗanda suka nuna goyon baya gareta.

"Ina matukar alfaharin kasancewa ƴar Najeriya. Na samu goyon baya sosai daga mai girma shugaban ƙasa, shugaban ma,aikata, ministan harkokin ƙasashen waje, ministan masana'antu, kasuwanci da zuba hannun jari.

"Ministocin sun yi aiki tuƙuru don ganin na samu nasara," a cewar Okonjo-Iweala.

"Shugaban ƙasa ya sakani farin ciki, ina alfahari da ƙasata," a cewarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel