Kwara: Mai mota ya buge Ango da Abokinsa su na kan babur ranar daurin aure

Kwara: Mai mota ya buge Ango da Abokinsa su na kan babur ranar daurin aure

- Wani hadarin mota ya ci kafafun Ango a birnin Ilorin da ke jihar Kwara

- A dalilin wannan hadari, wani mutum da ya halarcin bikin auren ya mutu

- Jami’an tsaron sun tabbatar da cewa an yi wannan hadari a ranar Lahadi

Wani Bawan Allah da ya zo bikin daurin aure ya gamu da ajalinsa bayan da mota ta auka masa a jihar Kwara, jaridar Punch ta rahoto wannan.

Jaridar ta bayyana cewa wannan labari mara dadin ji ya auku ne ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2020, a kan titin Ibrahim Taiwo, jihar Kwara.

Yayin da wannan mutumi da ya halarci bikin ya mutu a dalilin hadarin katuwar motar, angon ya gamu da mummunan rauni a kafafunsa biyu.

KU KARANTA: Ministan Tarayya ya sha da kyar a hannun 'Yan daba

Rahotanni sun tabbatar da cewa bakon da kuma angon su na kan babur da kimanin karfe 1:00 na rana, lokacin da wata mota ta auko masu ta baya.

Wannan mota kirar ‘Jeep’ ta murkushe wanda aka goya a babur, ta yi masa raga-raga da kwakwalwa, sannan ta raunata kafafun angon.

Angon shi ne wanda ya ke tuka babur din, motar ta karya masa duka kafafu biyu kamar yadda wanda aka yi hadarin a gaban idanunsa ya bayyana.

A lokacin da hadarin ya auku, angon ya na kokarin kai bakon na sa zuwa tashar da ke titin Wahab Folawiyo domin ya nemi mota, ya koma Legas.

KU KARANTA: Ana zargin Bola Tinubu da rashin biyan harajin N100bn

Kwara: Mai mota ya buge Ango da Abokinsa su na kan babur ranar daurin aure
Kwamishinan 'Yan Sanda, Kayode-Egbetokun
Asali: UGC

Marigayin ya zo garin Ilorin taka-nas ne domin ya halarci wannan daurin aure na abokinsa. A karshe wannan biki ya yi sanadiyyar barinsa Duniya.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar wannan hadari. Ya ce an yi gaba da motocin zuwa ofishin 'yan sanda tuni.

Yanzu nan kuma mu ke samun labari cewa wasu masu zanga-zanga sun kai hari a ofishin 'yan sanda, har ta kai an harbi jami'an tsaro da ke kan aiki.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Legas, Muyiwa Adejobi ya sanar da cewa an harbe jami'ansu. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel