Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri

Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri

- Karo na farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi kan soke rundunar yan sandan SARS

- Buhari ya bayana hakan a matsayin matakin farko na sauye-sauye masu tsauri da zai aiwatar kan aikin yan sanda

- Ya kuma sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an rundunar SARS da aka soke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, ya yi jawabi karo na farko kan soke rundunar yan sandan SARS.

A wani jawabi mai tsawon kimanin mintina biyu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kasar ya ce soke rundunar matakin farko ne a sauye-sauye masu kamari da zai aiwatar kan aikin yan sanda.

Ya e zai yi hakan ne don tabbatar da ganin cewa jami’an tsaro sun yi aikin da ya kamata da ba rayuka da dukiyoyi kariya.

Shugaban kasar ya ce za a hukunta jami’an rundunar da aka soke wadanda aka samu da aikata laifi.

Buhari ya kuma yi umurnin bincike a kan kisan wani matashi a jihar Oyo yayin zanga-zangar da aka gudanar kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Mazauna Pegi sun rufe kofar ofishin Ministan Abuja, sun fara zanga zanga

Ya kuma ce gwamnatin Najeriya ta damu da koken yan kasar kan amfani da karfi fiye da kima da yan sanda ke yi tare da kisa mara dalili.

Har ila yau Shugaban kasar ya ce aikin dan sanda shi ne ya kare yan kasa saboda haka ba za a lamunci wasu yan kadan ko bata gari su kasara kimar aikin ba a Najeriya.

Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri
Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Ya ce: “Soke rundunar SARS mataki na farko ne a sauye-sauye masu tsauri na yin garambawul a aikin yan sanda domin tabbatar da cewar aiki muhimmin aikin yan sanda da sauran hukumomin tsaro shine kare rayuka da dukiyoyin jama’armu.

“Za mu tabbatar da ganin cewa an hukunta wadanda ake zargi da hannu a cin zarafi.

“Mun yi bakin ciki da rasa ran wani matashi a jihar Oyo a yayin zanga-zangar kwanan nan.

“Na yi umurnin bincike a kan abunda ya haddasa mutuwarsa.

“A halin yanzu, yana da matukar muhimmanci mu gane cewa mafi yawancin jami’an rundunar yan sanda sun kasance hazikai sannan suna jajircewa kan aikinsu."

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ya rasu

Idan za ku tuna, Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.

Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng