Dr. Okonjo-Iweala ta sa labule da Shugaban kasa Buhari kan takarar WTO

Dr. Okonjo-Iweala ta sa labule da Shugaban kasa Buhari kan takarar WTO

- Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta kai ziyara ta musamman zuwa fadar Shugaban kasa

- Ana tunanin tsohuwar Ministar ta na ganawa ne da Buhari kan takararta a WTO

- Ministocin Tarayya ne su ka yiwa Okonjo-Iweala iso wajen shugaban kasar a dazu

Mun samu labari cewa tsohuwar Ministar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta iso fadar shugaban kasa na Aso Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta sa-labule da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau.

Rahotanni sun tabbatar da cewa karamin ministan harkokin waje, Amb. Zubair Dada; da kuma na sha’anin kasuwanci, Niyi Adebayo ne su ka yi mata iso.

Karamar ministar kasuwancin Najeriya, Hajiya Maryam Katagum ta na cikin wannan tawaga.

KU KARANTA: An ware N10.5bn domin ayi wa fadar Shugaban kasa kwaskwarima

Ngozi Okonjo-Iweala mai neman shugabancin kungiyar WTO ta kawowa shugaban kasar ziyara ne bayan ta samu kai wa zagaye na karshe na takarar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito karara ya nuna goyon bayansa ga tsohuwar Ministar.

A ranar Alhamis da ta wuce, gwamnatin tarayya ta yi kira ga ‘ya ‘yan WTO su goyi bayan Okonjo-Iweala a takarar da ta shiga na zama shugabar kungiyar.

Okonjo-Iweala ta rike kujerar Ministar kudi da kuma ta tattalin arziki a lokacin da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan su ke mulkin Najeriya.

KU KARANTA: ASUU ta maidawa Buhari martani kan barazanar albashi

Dr. Okonjo-Iweala ta sa labule da Shugaban kasa Buhari kan takarar WTO
Dr. Okonjo-Iweala Hoto: Twitter/NOIweala
Asali: Twitter

Katagum ita ce shugabar yakin neman zaben Okonjo-Iweala a WTO, Ministar ta bayyana ‘yar kasarta a matsayin wanda ta fi dacewa ta ja ragamar kungiyar.

A yanzu babu wanda ya sa wainar da ake toyawa tsakanin shugaban kasar da fitaciyyar masaniyar tattalin, wanda ta taba rike mukami a bankin Duniya.

A makon jiya kun ji cewa Okonjo-Iweala da Myung Hee sun zarce zuwa matakin zaben karshe a WTO. Tsakanin matan biyu ne za a samu wanda za ta rike WTO.

A bana kungiyar WTO za ta samu shugaba mace ta farko tun kafuwarta a shekarar 1995.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel