Yanzu yanzu: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ya rasu
- Allah ya yi wa shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara rasuwa
- An sanar da labarin mutuwar nasa ne a yau Litinin, 12 ga watan Oktoba
- Marigayin ya rasu ne a kasar Jamus inda ya ke jinya
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau, ya rasu.
An sanar da labarin mutuwar nasa ne a yau Litinin, 12 ga watan Oktoba.
Babban daraktan wayar da kai da watsa labarai na fadar gwamnatin jihar, Yusuf Idris ya tabbatar da rasuwar nasa, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito
Ya bayyana cewa marigayin mai shekaru 59 ya rasu ne a kasar Jamus bayan ya fama da ciwon koda wanda ake masa wankinta kafin liktoci su tabbatar da rasuwar tasa.
KU KARANTA KUMA: Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari

Asali: Twitter
“Shekaru 10 da suka gabata, ya taba zuwa kasar Indiya saboda matsalar, amma a wannan karon sai ya yanke shawarar zuwa Jamus domin samun kulawa, a nan ne kuma Allah Ya karbi ransa”, cewar Alhaji Yusuf.
Ya rasu ya bar mata hudu da ’ya’ya da kuma jikoki.
Ana sa ran yin jana’izarsa da zarar gawarsa tai so Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi
A wani labarin na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci iyalan Yar'adua bisa rasuwar Hajiya Rabi, surukar abokinsa, marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua, a jihar Kaduna.
Buhari ya siffanta mutuwarta a matsayin babban rashi.
Shugaban kasa, wanda ya tafi Kaduna ranar Laraba domin halartan bikin yaye daliban jami'ar horar da Sojoji NDA, ya dauki lokaci domin ziyartar iyalan Yar'aduan a gidansu.
Shugaban kasa, wanda ya tafi Kaduna ranar Laraba domin halartan bikin yaye daliban jami'ar horar da Sojoji NDA, ya dauki lokaci domin ziyartar iyalan Yar'aduan a gidansu.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, yayi a Abuja, ya ce shugaba Buhari ya samu tarba daga wajen Hajiya Binta Yar'adua, matar marigayi Shehu Musa Yar'adua da diyar Hajiyar da ta rasu.
Buhari ya ce Hajiya Rabi ta yi rayuwa mai albarka kuma ta yi tasiri matuka kan wadanda sukayi rayuwa da ita. Ya yi addu'a Allah ya karbi ibadunta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng