2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa

2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa

- Hauwa Atiku Uwais, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta sanar da duniya cewa zata ba wa mahaifin ta cikakken goyon baya idan ya fito takarar shugaban kasa a 2023

- A wani taro da aka yi a Abuja, Hauwa tace Allah ya albarkaci Najeriya da abubuwan amfani iri-iri, amma 'yan Najeriya sun fi kowa wahala, ga kuma tabarbarewar harkokin tsaro da suka addabi kowa

- Tace tana neman goyon bayan 'yan Najeriya wurin ganin an fita daga kangin rayuwa, duk da kasancewar mahaifinta attajiri, tana fita fafutukar neman rufin asirin rayuwa

Dangane da zaben 2023 dake tunkarowa, Hauwa Atiku Uwais, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tayi alkawarin mara wa mahaifinta baya, indai har ya sake neman takarar shugaban kasar Najeriya.

Hauwa ta bayyana hakan ne jiya a Abuja, lokacin da ake wata tattaunawa akan yadda za'a kawo gyara da cigaban Najeriya.

Hauwa ta nuna alhininta akan tabarbarewar al'amuran kasa, inda ta roki 'yan Najeriya da su dinga shiga cikin tattaunawar da zata haifar da 'da mai ido a Najeriya.

Manyan 'yan siyasa kamar Hon. Shaba Ibrahim, dan majalisar dake wakiltar mazabar Lokoja, kuma shugaban matasa, sun samu damar halartar taron.

Tace: "Kada ku yi wani kuskure! Zan tabbatar na bai wa mahaifina cikakken goyon baya, idan har ya fito neman kujerar shugaban kasa."

Tace, "Allah ya albarkaci Najeriya da abubuwan more rayuwa da dama, amma me yasa muka fi kowa wahala?

"Yanzu haka muna kokarin yin maja da duk wani mai neman cigaban kasa, muna da damuwa mai tarin yawa.

"Gaskiya idan bamu tsaya tsayin-daka ba, zamu yi ta wahala ne kawai. Muna bin hanyoyin da ba za su kaimu ko ina ba.

"Ku kalli yadda harkokin tsaro suka lalace, rayuka na hatsari a cikin shekaru 60 da Najeriya tayi da samun 'yancin kai."

Tace duk da mahaifinta, Atiku babban attajiri ne, amma duk da haka tana fafutukar neman samun abinda za ta rufawa kanta asiri, kamar yadda 'yan Najeriya da dama sukeyi.

KU KARANTA: EndSARS: Abubuwa 5 da IGP ya sanar yayin soke rundunar SARS

2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa
2023: Diyar Atiku Abubakar ta bayyana wanda za ta goyi baya ya shugabanci kasa. Hoto daga Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Korarren kwamishinan Ganduje ya yi martani a kan dakatar da Dawisu Yakasai

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi rayuwa tagari saboda su samu damar shiga aljanna.

Obasanjo ya sanar da hakan ne a wani taron hadin kai da aka yi na wata Majami'a da ke Ogba a jihar Legas.

An yi taron ne domin mika godiya ga Ubangiji a kan nasarar da aka samu wurin birne Olufunsho Salako, matar tsohon dan majalisar wakilai, Apostle Dave Salako.

Olufunsho ta rasu a ranar Lahadi, 9 ga watan Disamban 2020 tana da shekaru 59 a duniya sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel