Fadar Aso Villa za ta ci N10bn wajen gyare-gyare da aikin wuta a shekarar badi
- Najeriya za ta kashe N4.8m wajen kayan wutar lantarki a shekara mai zuwa
- Gwamnatin tarayya ta ware wasu miliyoyin kudi domin sayen man janareto
- Akwai shirin kashe kusan miliyan 60 wajen hawa shafukan yanar gizo a 2021
Fadar shugaban kasar Najeriya watau Aso Villa za ta kashe Naira biliyan 4.85 domin gyaran kayan wuta a 2021, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an ware Naira biliyan 5.3 da nufin yin wasu ‘yan gyare-gyare da kwaskwarima a ofisoshi da gidajen da ke cikin Aso Villa.
Wannan duk ya na cikin abin da aka shirya a kundin kasafin kudin shekarar 2021 wanda shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisa a makon jiya.
KU KARANTA: Atiku Abubakar ya ci gyaran Gwamnatin Buhari game da kasafin 2021
Wadannan kudi su na kan layin ERGP 7102245 annual routine maintenance of mechanical/electrical installations of the Villa a kundin kasafin badi.
Bayan N4, 854, 381, 299 da za a batar wajen aikin wuta, fadar shugaban kasar za ta ci N153, 693, 262 a gyaren dakuna da N5, 244, 027, 241 a kan ofisoshi.
Naira miliyan 5.2 za su tafi wajen gyaran injin janareto a shekara mai zuwa. Bayan haka gwamnatin tarayya za ta batar da Naira miliyan 45 wajen mai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware Naira miliyan 274 domin biyan kudin shan wutar lantarki da Naira miliyan 67.1 na hawo shafukan yanar gizo.
KU KARANTA: Kudin lantarki: ‘Yan kwadago sun yi zama da Gwamnati a Aso Villa
Gwamnatin tarayya ta yi wannan lissafi ne a lokacin da ta ke kukan rashin kudi, har ma ana tunanin tattalin arzikin Najeriya zai iya dakushewa a shekara mai zuwa.
A shekarar 2021, Gwamnatin Najeriya ta ci babban buri na kashe makudan kudin da ba ta taba batarwa ba. Muhammadu Buhari ya yi kasafin N13.08tr a 2021.
A kasafin kudin na badi, shugaba Buhari ya bayyana dalilin karin kudin fetur da lantarki. Gwamnati ta na kukan cewa ta na fama da karancin kudi.
Ku na da labari cewa bashin da ake shirin karbowa a 2021, ya zarce 3% na karfin GDP.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng