Ina tare da rundunar SARS don suna da muhimmancin gaske a kasar nan – Gwamna Matawalle

Ina tare da rundunar SARS don suna da muhimmancin gaske a kasar nan – Gwamna Matawalle

- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya nuna adawa da kiran a soke rundunar SARS

- Matawalle ya ce rundunar SARS na da muhimmancin gaske a kasar

- Ya alakanta kiran da wasu ke yi na a ruguza rundunar da son boye laifukansu

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya soki zanga-zangar da dandazon yan Najeriya suka yi na neman a ruguza rundunar SARS, ya ce ‘hakan ba alheri bane a gare mu’.

Mai magana da yawun gwamnatin Zamfara, Zailani Bappa a wata sanarwa da ya fitar da yawun Matawalle, ya ce gwamnan jihar baya tare da masu yin wannan zanga-zanga.

KU KARANTA KUMA: Atisayen Sahel Sanity: Dakarun soji sun kakkaɓe ƴan ta'adda a shiyyar Arewa maso Yamma

Ina tare da rundunar SARS don suna da muhimmancin gaske a kasar nan – Gwamna Matawalle
Ina tare da rundunar SARS don suna da muhimmancin gaske a kasar nan – Gwamna Matawalle Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Ya ce: “Ina tare da cigaba da aiki da rundunar SARS dari bisa dari domin mu a Zamfara mun san kokarin da suke yi mana.

“Duk wanda kuka ga yana adawa da SARS, toh ina mai baku tabbacin cewa bai da gaskiya, ko kuma akwai wani abu na rashin gaskiya da yake yi kuma SARS na takura masa.

“Ina kira ga gwamnatin tarayya da kada ta yi kuskuren sauraran masu wannan zanga-zanga, kada ta rusa SARS."

Sai dai kuma kuka da kiran Matawalle bai isa kunnen gwamnati da wuri ba.

Domin Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.

Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Abubuwa 5 da IGP ya sanar yayin soke rundunar SARS

Wannan na dauke ne cikin wata jawabi da ya yi kai tsaye a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoban 2020.

Sanarwar na zuwa ne bayan al'umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna da kuma dandalin sada zumunta na neman a soke rundunar a kasar baki daya don kisa da cin zarafin al'ummma da suke yi.

Yayin jawabin, IGP ya ce, "An soke Rundunar tarayya ta musamman masu yaki da fashi da makami da aka fi sani da SARS a dukkan rundunonin 'yan sanda da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel