EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo

EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo

- Hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu ya yi magana a kan SARS

- Baya ga haka, hadimin gwamnan Kanon ya yi wa shugaban kasa Buhari wankin babban bargo a kan halin da ya nuna

- Ya bayyana cewa bai taba ganin gwamnati mara tausayin 'yan kasa ba kamar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari

Mai bai wa Gwamna Ganduje shawara na musamman a fannin yada labarai, Salihu Tanko, a ranar Lahadi ya goyi bayan zanga-zangar da ake wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cin zarafin da 'yan sanda ke yi.

Hadimin ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rikon sakainar kashi ga muhimman al'amura da suka shafi 'yan Najeriya.

Tanko a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter da kuma tattaunawa da yayi da jaridar Premium Times, ya ce shugaban kasar ya ci amanar wadanda suka zabesa kuma ya watsa wa magoya bayansa kasa a ido har da shi.

Tanko ya wallafa a Twitter, "Ban taba ganin gwamnati da bata da tausayi ba kamar ta shugaban kasa Buhari. Sau da yawan lokuta idan jama'arsa suna fuskantar matsala, a maimakon ya tausasa musu tunda shine bangonsu, sai ya kasa hakan.

"Yadda yake nuna bai damu da al'amuran jama'a ba yayi yawa," Tanko ya wallafa.

Ya kara da cewa, "Yi wa jama'arka jawabi a kan abinda ke matukar damunsu ya zama tamkar wata alfarma da za ka yi musu."

"Har kullum, ba za ka iya bada minti biyar kacal ba domin kwantarwa jama'arka hankali. Ka iya zagaye jama'ar da ka bi jihohi 36 don rokonsu kuri'unsu. Wannan abun takaici ne," ya wallafa.

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo
EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo. Hoto daga @Dawisu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe

Tanko ya sanar da Premium Times cewa zanga-zangar da ake yi har yau shugaba Buhari bai mayar da hankali ba.

"Kafin zanga-zangar akwai matsalolin tsaro da ke addabar arewa da kuma wasu manyan ayyuka da ya kamata shugaban kasa ya bada hankalinsa domin ganin sun kammala, amma yayi shiru.

"A matsayina na dan kasa kuma mai goyon bayan shugaban kasa, ba za mu cigaba da kalmashe hannu muna ganin abinda za a yi nadama a nan gaba yana faruwa ba," Tanko yace.

A wani labari na daban, Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa, ya daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin wata babbar kotun tarayya wacce ta ci tararsa naira miliyan 50 a kan cin zarafin wata mata.

A 2019, 'yan sanda sun gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, a kan zarginsa da laifin cin zarafin wata mata mai suna Osimibibra Warmate a wani shago a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel