Ba ma yi: Mutane 100,000 sun yi wa Buhari tawaye a shafukansu na Twitter

Ba ma yi: Mutane 100,000 sun yi wa Buhari tawaye a shafukansu na Twitter

- Masu amfani da shafin Twitter dubu dari sun yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tawaye

- Hakan na daga cikin matakin da suka dauka domin ganin an kawo karshen ayyukan yan sandan SARS

- Yan Najeriyan dai sun daina bin shafin shugaban kasar na Twitter

Kimanin masu amfani da shafin Twitter dubu dari ne suka daina bin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan shafin na dandalin sada zumunta.

Hakan na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya kaddamar da wata kafen na daina bin Shugaban kasar a shafin wato #UnfollowBuhari.

A cewar Omokri, hakan zai taimakawa kiran da ake na kasa baki daya a kan kawo karshen rundunar yan sandan SARS da ake zargi da kashe matasan Najeriya da basu ji ba basu gani ba.

Ba ma yi: Mutane 100,000 sun yi wa Buhari tawaye a shafukansu na Twitter
Ba ma yi: Mutane 100,000 sun yi wa Buhari tawaye a shafukansu na Twitter Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Buhari wanda ke da kimanin mabiya miliyan 3.5 kuma yake bin mutum 26, a yanzu yana da mabiya miliyan 3.4 sannan yana bin mutum 26.

Hakan na nufin mabiyansa sun ragu da kimanin 100,000, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yan Najeriya sun fara kira ga neman a soke ayyukan rundunar SARS, wadanda ke cin zarafin matasa da dama a lokuta da dama.

KU KARANTA KUMA: Zaben Ondo: PDP ta lallasa APC da tazarar ƙuri'u mai yawa a ƙaramar hukumar Akure

Domin daukaka muryoyinsu a kan haka, yan Najeriya manya da kana, da masu fada a aji sun shiga unguwanni domin zanga-zangar kawo karshen SARS.

Sun yi kira ga Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu da shugaba Buhari a kan su kawo karshen ayyukan SARS.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS

A gefe guda, sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da ya bayar ta kafar talabijin a ranar Lahadi. Sanarwar na zuwa ne bayan al'umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel