KAI TSAYE: Yadda zaben jihar Ondo yake gudana
A yau Asabar, 10 ga watan Oktoban 2020, jama'ar jihar Ondo za su kada kuri'unsu domin zaben gwamna na 7 a cikin shekaru 44 da kafuwar jihar.
Legit.ng za ta dinga kawo muku rahoto dalla-dalla kai tsaye daga jihar Ondo.
A zaben yau, jam'iyyyun siyasa 17 wadanda suka hada da APC da PDP duk sun fitar da 'yan takararsu.
Masu ruwa da tsaki a jihar sun bayyana tsoronsu na yuwuwar rikici, ganin cewa akwai tarihin rikicin zabe da tashin-tashina a jihar.
An kammala jefa kuri'a a wasu rumfunan zabe, an fara kidaya
An kammala jefa kuri'a kuma an fara kidaya yanzu haka a rumfar zabe mai lamba 02, gunduma ta 4 a Idanre lGA (TheCable)
An kammala jefa kuri'a kuma an fara kidaya yanzu haka a rumfunan zabe da dama dake gunduma ta 06 a karamar hukumar Akoko Northwest
An kama masu sa ido kan zabe na bogi da ake zargin Jam'iyyar PDP suka yi wa aiki a Ondo
An cafke wasu masu sa ido kan zabe na bogi da ake zargin jam'iyyar PDP suke yi wa aiki a yankin Ijomu a Akure ta jihar Ondo.
Mai kada kuri'a ya yanke jiki ya fadi a layin zabe
Wani mai kada kuri'a a gunduma ta 10 da ke Oke-Otunba, rumfa ta 7 da ke MDS Ododigbo/Okedibo II, ya yanke jiki ya fadi a layin zabe.
An gano cewa mai kada kuri'ar yana fama da farfadiya.
Dan takaran gwamnan PDP, Eyitayo Jegede, ya kada kuri’ar
Mataimakin gwamnan jihar Ondo kuma dan takarar gwamna na ZLP, Ajayi ya kada kuri'arsa
Mataimakin gwamna kuma dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar ZLP, Agboola Ajayi a rumfar zabensa ta Kiribo da ke karamar hukumar Ese Ondo a jihar Ondo.

Asali: Twitter
Tsirarun masu zabe sun fara kada kuri'a bayan ruwan sama ya tsagaita a Ondo
Masu zabe sun fara dawowa don cigaba da kara kuri'unsu bayan ruwan sama ya tsagaita a Ondo.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Wasu wakilan jam'iyyun siyasa sun fara sayan kuri'a a garin Illaje na jihar Ondo
Wasu wakilan jam'iyyun siyasa sun fara sayan kuri'a a garin Illaje
@CDDWestAfrica ce ta gano siyan kuri'un
@MatthewTPage ya ce irin wannan lamarin ya saba faruwa a garuruwan da ke da wuyan zuwa

Asali: Twitter
Dan majalisa Olubunmi ya isa rumfar zabensa da ke Akoko
Olubunmi Tunji-Ojo, shugaban kwamitin majalisar wakilai na NDDC, ya isa rumfar zabensa ta 13,, gunduma ta 3 da ke karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma a jihar.

Asali: Twitter
Gwamna Rotimi Akeredolu ya kada kuri'ansa

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Gwamnan Akeredolu ya isa rumfar zabensa da ke Ijebu Owo tare da matarsa
Gwamnan jihar Ondo, kuma dan takara a karkashin jam'iyyar APC, Akeredolu Rotimi, ya isa rumfar zabensa tare da matarsa a Ijebu Owo.

Asali: Twitter
Jami'an tsaro a kan babura za su kai kayayyakin zabe rumfar zabe a Akure-Owo road a jihar Ondo

Asali: Twitter
Dan takarar PDP, Jegede tare da matarsa sun isa rumfar zabensu
Dan takarar gwamnan jihar Edo, karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya isa rumfar zabensa mai lamba 9 a gunduma ta 2 da ke karamar hukumar Akure ta Kudu.
Ruwan sama ya tarwatsa masu kada kuri'a a karamar hukumar Akure ta arewa
Akwati na 7 a gunduma ta 2 ta karamar hukumar Akure ta arewa, jama'a sun fara kada kuri'a amma ruwa ya tarwatsasu inda suka bazama neman mafaka.

Asali: Twitter
Ma'aikacin wucin-gadi yana wayar wa da masu kada kuri'a kai
A Agba, akwati na 08, gunduma ta 4 da ke karamar hukumar Akoko ta kudu masu yamma, shugaban akwatin zaben yana wayar wa masu kada kuri'a kai kafin fara zaben.

Asali: Twitter
Ma'aikatan zabe sun fara lika rijistar wadanda za su yi zabe
Ma'aikatan zabe sun fara isa rumfunan zabe inda suke lika rijistar wadanda za su yi zabe.

Asali: Twitter

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng