'Yan bindiga sun harbe dan majalisa yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa

'Yan bindiga sun harbe dan majalisa yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa

- Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashi da makami ne sun harbe dan majalisar dokokin kasar Ghana

- An harbe dan majalisar ne yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa

- Ana shirin sake gudanar da zabe a kasar Ghana a cikin watan Disamba mai zuwa

'Yan sanda a kasar Ghana sun bayyana cewa sun fara binciken kisan wani dan majalisar dokokin kasar da aka yi ranar Juma'a yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa.

Ana zargin cewa 'yan bindigar sun harbe dan majalisa mai suna Ekow Quansah a kokarinsu na yi ma sa fashi.

Honarabul Ekow Quansah, mamba a jam'iyyar NPP ta shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma'a a mazabarsa mai nisan kilomita 108 daga Accra, babban birnin kasar Ghana.

DUBA WANNAN: PSC ta kori ACP da sauran wasu manyan jami'an 'yan sanda 9, an ragewa 9 mukami

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa Honarabul Quansah ya ziyarci mazabarsa ne domin halartar taron siyasa gabanin zaben da za a yi a kasar Ghana a cikin watan Disamba.

"Direbansa ya yi kokarin kaucewa shingen kan hanyar da aka saka amma 'yan bindigar su ka harbeshi," kamar yadda Wofa Yawa, shugaba a NPP, ya sanar da AFP.

'Yan bindiga sun harbe dan majalisa yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa
Shugaban kasar Ghana da Buhari a Najeriya
Asali: Twitter

A cikin wani jawabin da ya fitar, babban sifeton rundunar 'yan sandan Ghana, Oppong-Boanuh, ya ce tuni an tura jami'ai na musamman ma su bincike zuwa yankin da aka kashe dan majalisar domin gano wadanda su ka kashe shi.

DUBA WANNAN: Zaben gwamna: An bukaci gwamnoni su gaggauta fita daga jihar Ondo

Kazalika, ya bayyana cewa jami'an za su taimaka wajen kawo karshen miyagun aiyuka, musamman fashi da makami, da ake yi a yankin.

Shugaban kasar Ghana ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalin dan majalisar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

"Bisa ga dukkan alamu, jama'ar mazabarsa su na matukar kaunarsa. Ina tsammanin jami'an 'yan sanda za su nemo 'yan ta'addar da su ka kashe shi tare da gurfanar da su idan hakan mai yiwuwa ne," a cewar shugaba Akufo-Addo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel