Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

- Karfin hali ya kai wani matashi mai suna Kabiru shiga majalisar dokoki sata

- Bai sani ba ashe na'urar CCTV na daukansa yayinda yake satan

- Tuni an damke shi kuma an sanar da jami'an tsaron majalisar dokokin dake Abuja

Wani matashi mai suna Kabiru a ranar Juma'a ya fasa cikin majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki.

Wannan abu ya faru misalin karfe 2:30 na rana inda matashin yayi amfani wani mukulli na daban.

An yi zargin Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu na'urar kwamfuta, na'urar fotocofi da printer.

SaharaReporters ta tattaro cewa Kabiru ya kasance hadimi ga wani dan majalisa daga Adamawa kuma sannanen mutum ne a majalisar.

Jami'an tsaron majalisar sun gane fuskarsa a bidiyon na'urar CCTV da ta daukeshi yana fashin.

A yayinda ake tattara wannan rahoton, wasu yan majalisa wanda ya hada da mai magana da yawun mambobin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, na wajen da aka kama matashin.

An samu labarin cewa dan majalisar da matashin ke yiwa aiki yana kokarin ganin an yi rufa-rufa kawai a manta da lamarin.

Bidiyon na'urar CCTV ya nuna matashin lokacin da yake satan.

KARANTAN WANNAN: Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar

Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki
Credit: @saharareporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Najeriya fa kamar mota ce mara matuki (direba) - Attahiru Jega da sauran manya

A wani labarin mai tashe, Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa, ya daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin wata babbar kotun tarayya wacce ta ci tararsa naira miliyan 50 a kan cin zarafin wata mata.

A 2019, 'yan sanda sun gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, a kan zarginsa da laifin cin zarafin wata mata mai suna Osimibibra Warmate a wani shago a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel