Kai tsaye: Nigeria 0-1 Algeria (Wasan kwallon sada zumunta)

Kai tsaye: Nigeria 0-1 Algeria (Wasan kwallon sada zumunta)

An fara wasan sada zumuntan Nigeria vs Algeria daidai karfe 7:30 na dare.

Wasan karshe da bangarorin biyu suka buga shine wasan kusa da karshe a gasar kasashen nahiyar Afrika inda Algeria ta lallasa Najeritta da 2-1.

A tarihi kuwa, Najeriya da Aljeriya sun doki juna sau tara-tara.

An sake canji

Samuel Chukwueze ya fita, Ahmad Musa ya shigo

An sake canji

Samuel Kalu ya fita, Simon Moses ya shigo

An kusa dawowa hutun rabin lokaci, Mike Agu motsa jiki

Zai maye gurbin sabon dan wasa Frank Onyeka idan aka dawo

an tafi hutun lokaci

HT: Nigeria 0-1 Algeria.

Ramy Bensebaini ya zura kwallo daya ragar Najeriya

Online view pixel