Zaben gwamna: An bukaci dukkan gwamnoni su fice daga jihar Ondo
- A gobe, Asabar, 10 ga watan Oktoba, hukumar zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo
- Bisa al'adar siyasar Najeriya, gwamnonin kan yi taron dangi a duk jihar da za a gudanar da zaben kujerar gwamna daga baya
- Gamayyar wasu kungiyoyi fiye da 200 sun bukaci dukkan gwamnonin da su ka hauro zuwa Ondo su fice daga jihar tunda an gama kamfen
A yayin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kammala shirin gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Ondo, gamayyar kungiyoyi fiye da 200 a karkashin tutar TMG (Transition Monitorin Group) sun fitar da jawabi mai karfi da yammacin Juma'a.
TMG ta bukaci INEC ta samar da na'urar Z-pad mai amfani da fasahar zamani domin samun damar aika sakamakon zabe kai tsaye daga akwatuna 3,009 da ke mazabu 203 a kananan hukumomi 18 da ke jihar Ondo.
KARANTA: Pantami ya bayyana gatan da FG za ta yi wa mazauna IDPs ta hannun ma'aikatarsa
Shugabar kungiyar TMG, Dakta Abiola Akiyode Afolabi, ce ta fadi hakan yayin wani taron hadin gwuiwa da kungiyar NAPEN mai rajin neman a gudanar da zabe cikin zaman lafiya.
Da ta ke gabatar da jawabi yayin taron, Dakta Afolabi ta yi Alla-wadai da dabi'ar taron dangi da gwamnoni ke yi a duk jihar da za a yi zaben gwamna daga baya.
KARANTA: PSC ta kori ACP da sauran wasu manyan jami'an 'yan sanda 9
"Sun baro jihohinsu tare da yin amfani da kudin jama'arsu wajen zuwa jihar Ondo domin razana jama'a ta hanyar amfani da dumbin jami'an tsaron da su ke biye dasu.
"Su ne ke assasa magudi da sauran laifukan zabe irinsu sayen kuri'a, firgita ma su zabe ta hanyar amfani da jami'an tsaro da kuma daukan nauyin matasa 'yan daba da ake amfani da su wajen tafka magudin zabe," a cewar shugabar TMG
Kazalika, kungiyar ta bukaci ''dukkan gwamonin da su ka hauro zuwa cikin Ondo'' su bar jihar tunda an kammala yakin neman zabe.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng