Donald Trump ya ki yarda ya yi muhawara da ‘Dan takarar Republican, Joe Biden

Donald Trump ya ki yarda ya yi muhawara da ‘Dan takarar Republican, Joe Biden

- CPD ta canza tsarin yadda ake muhawarar ‘yan takarar Amurka saboda COVID-19

- Donald Trump ya nuna cewa ba zai muhawara da Joe Biden ba tare da sun hadu ba

- Wasu na ganin Shugaban dai ya na neman mafaka ne, akasin ra’ayin na-kusa da shi

A ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump, ya bayyana cewa ba zai yi muhawara da Joe Biden ta kafar na’ura ba.

An shirya muhawarar Donald Trump da Joe Biden ta zama ta talabijin ne bayan shugaban na Amurka ya kamu da cutar COVID-19 a makon da ya wuce.

“Ba zan yi muhawara ta bayan na’ura ba.” Trump ya shaidawa gidan Fox Business wannan a jiya.

KU KARANTA: Trump da Biden sun yi wa juna kaca-kaca a muhawarar farko

Trump ya ce in dai har zai yi muhawara, sai dai ya fito ga shi-ga mutum. “Ba zan bata lokaci da wata muhawara da ba a fili ba. Wannan ba muhawara ba ce.”

“Sai ka zauna a bayan gafaka, ka na muhawara, shiriri ta kenan.” Inji Shugaba Donald Trump.

A jiya hukumar CPD da ke shirya irin wannan zama ta bada sanarwar Donald Trump da Joe Biden za su gwabza a ranar 15 ga watan Oktoba, ba tare da sun hadu ba.

Shugaban yakin neman zaben Trump, Bill Stepien, ya yi watsi da sanarwar da hukumar CPD ta fitar a ranar Alhamis, ya na ganin babu bukatar irin wannan zama.

KU KARANTA: Trump ya tsorata bayan ya kamu da COVID-19

Donald Trump ya ki yarda ya yi muhawara da ‘Dan takarar Republican, Joe Biden
Donald Trump da Joe Biden Hoto: Vanguard
Asali: UGC

“Za a iya kare lafiyar kowa ba tare da an sauya yadda ake muhawara ba, mutane su samu damar ganin ‘yan takara ido-da-ido.” Inji shugaban yakin zaben Trump.

Mista Stepien wanda shi ma ya kamu da COVID-19 ya na ganin cewa sauya tsarin zaman wata dabara ce ta rufa wa Joe Biden asiri daga shan kunya a hannunsu.

Dazu kun ji cewa Jami’an FBI sun bankado yunkurin garkuwa da Gwamna Gretchen Whitmer a kasar Amurka, kuma har an kama masu kitsa wannan mugun nufi.

Wadannan Miyagu da aka kama su na zargin Whitmer da wasu Gwamnoni da kin bin dokar kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel