Yadda Gwamnatin Buhari za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa

Yadda Gwamnatin Buhari za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin 2021 a gaban Majalisa

- Ana sa rai a amince da kasafin kudin badi tun kafin shekarar bana ta shude

- Najeriya ta ci dogon burin kashe makudan kudin da ba ta taba batarwa ba

A ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2020, shugaban Najeriya ga gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 gaban ‘yan majalisar tarayya.

Mun kawo maku manyan abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan kasafi na badi:

1. Najeriya za ta batar da Naira tiriliyan 13

Shugaba Muhammadu Buhari ya na da burin kashe Naira tiriliyan 13.08 a shekara mai zuwa. Yanzu ya ragewa majalisar wakilai da dattawa su zauna a kan kundin kasafin.

2. Ayyukan more rayuwa sun ci 23%

A kasafin kudin na 2021, abin da aka warewa ayyukan more rayuwa shi ne 23.85%, ma’ana Naira tiriliyan N3.12 za su tafi wajen yin tituna, dogo, madatsan ruwa, da sauransu.

KU KARANTA: Babu IPPIS, babu albashi - Buhari ya fadawa ASUU

3. Albashin ma’aikata

Abin da za a kashe a matsayin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da alawus a shekara 2021 ya haura Naira tiriliyan 3.7%, kusan 28.75% zai kare ne a cikin ‘yan kwadago.

Abin da aka warewa fansho da kudin sallamar ma’aikatan gwamnati shi ne Naira biliyan 501.9.

4. Biyan bashi da aron kudi

A shekara mai zuwa, gwamnatin Najeriya za ta biya bashin Naira tiriliyan 3.12 da ke kanta. Bayan haka kuma za a sake nemo aron wasu kudin da su ka kusa kai Naira tiriliyan 5.

5. Kudin gangar mai

Najeriya ta sa ran cewa za ta rika saida gangar danyen mai a kasuwannin Duniya a kan fam Dala $40. An yi lissafin duk rana za a hako gangunan mai miliyan 1.86 a shekarar 2021.

KU KARANTA: Buhari ya godewa 'Yan Najeriya wajen gabatar da kasafin kudi

Yadda Gwamnatin Buhari za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa
Shugaba Buhari a Majalisa Hoto: Twitter/BashirAhmaad
Asali: Twitter

6. Kudin shiga

Abin da gwamnatin tarayya ta ke tunanin za ta samu a matsayin kudin shiga a badi shi ne Naira tiriliyan 7.886. Za a samu kudin ne daga mai, albarkartu, haraji, da gudumuwa.

7. Dalar Amurka

Gwamnatin kasar ta tsaida canjin Dala a kan N379 a shekarar 2021, ana sa rai kuma tattalin arziki zai motsa da 3%, an bar hauhawar farashin kaya a kan 11.95%.

A wajen gabatar da kasafin kudin, shugaban kasar ya bayyana matakin da zai dauka a kan hukumomin gwamnati da ke daukan ma'aikata ba tare da bin ka'ida ba.

Haka zalika Buhari ya bayyana cewa annobar COVID-19 ya awo faduwar farashin danyen mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel