Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare

Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare

- Rundunar soji ta sanar da samun nasarar cafke wani mutum da ke shigowa da kungiyar Boko Haram da ISWAP makamai daga ketare

- A cewar Manjo Janar John Enenche, an kama mutumin, dan asalin Najeriya, a jamhuriyar Nijar

- Enenche ya bayyana cewa kwalliya ta na biyan kudin sabulu a atisaye daban-daban da rundunar soji ta kaddamar a fadin Najeriya

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa jami'an soji na Atisayen lafiya dole sun kama wasu makamai na ƙasar waje tare da mai shigo da makaman ga ƴan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram da kuma ISWAP wadda ta ɓalle daga jikin Boko Haram.

Bayanan sun fito daga bakin shugaban sashen labarai na rundunar tsaro, Manjo janar John Enenche, lokacin da yake ƙarin haske game da irin nasarar da atisayen sojoji ke samu a ranar Alhamis a garin Abuja.

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'

Eneche ya ce mai laifin, wanda ya kasance ɗan asalin ƙasar Najeriya ne, an kama shi a kusa da sansanin ƴan gudun hijira a yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar a ranar 3 ga watan oktoba.

Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare
Manjo Janar John Enenche
Asali: Twitter

A cewar Enenche, rundunar soji ta yabawa dakarun sojoji a bisa samun wannan nasara da kuma sauran bajintar da su ke nunawa.

DUBA WANNAN: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu

Kazalika, ya bayyana cewa su na ƙarfafawa mutane guiwa da su cigaba da bada bayanai da za su taimakawa rundunar soji wajen samun nasara a kan 'yan ta'adda da yaki da ta'addanci a fadin kasa.

Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama mai laifin ne biyo bayan tattara bayanan sirri a kan ƴan ta'adda a ƙauyen Chinguwa dake ƙasar Nijar kusa da garin Gashigar a ƙaramar hukumar Mobbar dake Jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng