Buhari ya bayyana matakin da zai dauka a kan daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba

Buhari ya bayyana matakin da zai dauka a kan daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba

- A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2021

- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi N13.1trn a gaban mambobin majalisar tarayya yayin wani zama na musamman

- Buhari ya bayyana cewa annobar korona da faduwar farashin danyen mai ta nakasa tattalin arzikin Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi gargaɗin cewa dukkan wata hukumar gwamnati da ta ɗauki aiki ba tare da izini ba zata fuskanci hukuncin saka ma ta takunkumi.

Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne yayin da ya ke gabatar da ƙiyasin kasafin kuɗin shekarar 2021 a yayin taronsa da majalisa a babban birnin tarayyar Abuja a ranar alhamis.

Ya kuma shawarci ƴan-majalisar da su maida hankali kan kuɗaɗen shiga kamar yadda za su maida hankali wajen kasafi.

DUBA WANNAN: Rashin imani: An kone dan Najeriya 'kurmus' da ransa a kasar Libiya

Kasafin kuɗin bana zai maida hankali wajen tattara samun kuɗin shiga, duk ƙanƙantarsu, daga ma'aikatu, ƙananan ma'aikatu, da hukumomi.

Buhari ya bayyana matakin da zai dauka a kan daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba
Buhari ya yin gabatar da kasafin kudin 2021
Asali: Twitter

Yace kasafin kuɗin bana taswirar hanyar farfadowar ce bayan fama da annobar korona wadda za ta taimaka wajen saurin mikewar tattalin arziƙi cikin hanzari.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa bullar annobar korona ya taba tattalin arzikin Najeriya, sannan ya kara da cewa faduwar farashin danyen mai ta hana gwamnati samun isassun kudin shiga.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'

Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N13.1trn, hakan ya nuna cewa an samu karin kaso 20% a kan adadin kudin da gwamnati ta yi kasafi a baya.

A cewar Buhari, akwai gibin N4.8trn a cikin kasafin, wanda ya bayyana cewa gwamnati za ta cike gibin da rance daga ketare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel