Yanzu Yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

- Hankula sun tashi yayinda rikici ya kaure a yankin Igbo-Olomu na Ikorodu a jihar Lagas a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba

- Rikicin ya kasance a tsakanin matasan Hausawa da na Yarbawa

- Lamarin ya fara ne a lokacin da wani Bayarabe ya ki biyan dan achaba Bahaushe kudin daukarsa da yayi

An shiga rudani a yankin Igbo-Olomu na Ikorodu a jihar Lagas a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, yayinda matasan Hausawa da Yarabawa suka yi mummunan karo.

Yanzu haka wajen ya zama wayam ba mutane yayinda mazauna yankin suka tsere zuwa gidajensu bayan sun ga yadda aka dunga illata mutane da makamai, jaridar PM News ta ruwito.

KU KARANTA KUMA: Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas
Yanzu Yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Shaidu sun bayyana wa manema labarai cewa mummunan al’amarin ya fara ne a safiyar yau Alhamis, bayan wani fasinja Bayarabe ya ki biyan dan achaba Bahaushe kudin daukarsa da yayi.

Sai dai, wata majiya ta tsaro ta bayyana wa jaridar ta yanar gizo cewa an tura jami’an yan sanda yankin domin dawo da zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa

A wani labari na daban, masu zanga-zanga da ke bukatar a gyara tsarin 'yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami a fadin kasar nan sun zagaye hedkwatar 'yan sandan Najeriya da ke Abuja.

Masu zanga-zangar suna kan babbar hanyar Shehu Shagari inda suke ta ihun a kawo karshen SARS yayin da suka takaita kaiwa da kawowar ababen hawa.

A wannan halin, suna rike da takardu masu rubuce-rubuce daban-daban duk suna nuna bukatarsu, The Punch ta wallafa.

Masu zanga-zangar sun dinga watsa jan fenti a kan tituna domin nuna yadda jami'an SARS ke zubda jinii tare da kashe-kashe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel