Makinde da George su ka shirya abin da aka yi mani a jihar Ondo inji Fayose

Makinde da George su ka shirya abin da aka yi mani a jihar Ondo inji Fayose

- Ayodele Peter Fayose ya bayyana wadanda su ka sa aka cire masa hula a Ondo

- Tsohon gwamnan ya ce Bode George da Makinde ne su ka sa a wulakanta shi

- Amma Taiwo Adisa ya musanya wannan zargi a madadin Gwamnan Jihar Oyo

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Peter Fayose ya jefi wasu jiga-jigan PDP da laifin hannu a harin da aka kai masa a jihar Ondo.

Ayodele Fayose ya ambaci sunan tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Cif Bode George cikin wadanda su ka kitsa harin da aka kai masa.

Fayose ya ce akwai hannun mai girma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, a yunkurin ci masa mutunci da aka yi a babban gangamin PDP.

Tsohon gwamnan na PDP ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Lere Olayinka, ya na mai cewa duk da abin da ya faru, ba zai daina fadin gaskiya ba.

KU KARANTA: An ja-kunnen Fayose kan sukar Jagororin PDP

Jagoran adawar ya dade ya na rikici da Cif Bode George da kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Fayose ya na zargin Bode George da rashin nasarar da PDP ta ke samu a jihar Legas tun 1999, don haka ya ce ya kamata ayi wa ‘dan siyasar ritaya.

Lere Olayinka ya ce mai gidansa zai kai kara wajen jami’an tsaro da shugabannin jam’iyyar PDP da su ka dace domin a dauki matakin da ya kamata.

Makinde da George su ka shirya abin da aka yi mani a jihar Ondo inji Fayose
Fayose da Bode George Hoto: Punch/Sun
Asali: UGC

KU KARANTA: A tsare Magu yadda ya yi wa Jama'a - Fayose

Hadimin tsohon gwamnan ya ce lamarin ba abu ne na wasa ba, dole jami’an tsaro su gano wadanda su ka kitsa wannan aiki tare da bankado iyayen gidansu.

Sakataren yada labarai na gwamnan Oyo, Taiwo Adisa, ya fito ya yi martani, ya ce: “Fayose ya na neman suna ne kurum, gwamna ba zai biye masa ba.”

Seyi Makinde ta bakin Taiwo Adisa ya ce abin da ke gabansa shi ne karfafa PDP a yankin Kudu maso yamma, ba ya biyewa sambatun Ayo Fayose ba.

Idan za ku tuna wasu tsageru sun cire wa Fayose hula a lokacin da ya tashi zai yi jawabi a wajen babban taron da PDP ta shirya na kamfe a jihar Ondo.

Mista Fayose ya fito ya ce so ake a salwantar da rayuwarsa kamar yadda aka yi wa Bola Ige.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel