Mama Helina Metosudo Seth ta bar Duniya ta na da shekaru 118

Mama Helina Metosudo Seth ta bar Duniya ta na da shekaru 118

- A cikin farkon makon nan ne Helina Metosudo Seth ta rasu

- Helina Metosudo Seth ta bar Duniya ta na mai shekara 118

- Marigayiyar ita ce ta haifi Mataimakin gwamnan Adamawa

A ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, 2020, jihar Adamawa ta yi babban rashi na madam Mama Helina Metosudo Seth.

Marigayiya Mama Helina Metosudo Seth, mahaifiya ce wajen mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Cif Crowther Seth.

Mai girma Crowther Seth ya shaidawa ‘yan jarida cewa mahaifiyarsa, Helina Metosudo Seth ta rasu ne a makon nan.

KU KARANTA: Takaici ya sa Malamin makaranta ya rataye kansa har lahira

Kamar yadda jaridar The Nation ta fitar da rahoto, Mama Helina Seth ta cika ne a safiyar ranar Talatar da ta gabata.

Crowther Seth ya tabbatar da cewa Marigayiyar ta rasu ta na da shekaru 118 da haihuwa.

Yanzu an fara shirye-shiryen bizne Marigayiyar nan da mako biyu. Ta na cikin wadanda su ka fi tsufa a Najeriya.

Za a birne Helina Metosudo Seth a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, 2020, a gidansu na gado a garin Lamurde.

KU KARANTA: Donald Trump da sauran Shugabannin kasashen da COVID-19 ta harbe su

Mama Helina Metosudo Seth ta bar Duniya ta na da shekaru 118
Mama Seith Hoto: The Nation
Asali: UGC

Babban gidan mataimakin gwamnan ya na karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa.

Ba mu da labarin sauran ‘ya ‘ya da jikokin wannan Baiwar Allah, face cewa ita ce ta haifi mataimakin gwamnan mai-ci.

Crowther Seth Lauya ne, kuma ya na cikin masu ba jam’iyyar PDP shawara a kan harkar shari’a, kafin ya shiga siyasa.

A shekarar bara kun ji labarin wata tsohuwa 'yar shekara 100 da ta rasu tare da yayanta a wani kauye a jihar Ebonyi.

'Yan Sanda sun ce wadannan Bayin Allah hudu, sun mutu ne bayan sun ci guba a cikin abinci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel