Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa

Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa

- An nemi tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina an rasa

- Hakan ya sa an kunno wa Sanata Ali Ndume, wanda ya tsaya masa wuta a kan ya nemi soke lamunin da ya yi masa

- Ana dai tuhumar Maina da aikata zambar kudi har naira biliyan biyu

Ko sama ko kasa an nemi tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina da dansa Faisal an rasa.

An tattaro cewa an shigar da korafi ga hukumar tsaro na farin kaya (DSS) da rundunar yan sandan birnin tarayya domin su gano inda yake.

Hakan ya saka wanda ya tsaya wa Maina, Sanata Ali Ndume fuskantar matsin lamba na neman soke lamunin da yayi masa.

Maina, dansa da kamfanin Common Input Property and Investment Ltd na fuskantar shari’a a gaban Okon Abang na babbar kotun tarayya, Abuja kan zargin zambar kudi naira biliyan biyu.

An gurfanar da su kan tuhume-tuhume 12 da suka hada da damfara da sauransu.

Koda dai Sanata Ndume ya hallara a kotu, wanda ake zargin ya ki zuwa kotu a ranakun Juma’a, Litinin da Talata da suka gabata.

An tattaro cewa magana ta karshe da aka yi da Maina ya kasance a daren ranar Alhamis, lokacin da ya sanar da cewar zai halarci zaman kotu a ranar Juma’a da ta gabata.

Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa
Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Nan take sai aka sanar da ofishin yan sanda na Jabi domin su kama shi amma sai ba a a sake jin doriyar Maina ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa

Wata babbar majiya ta ce: “tun da ba a sake jin doriyarsa ba, an shigar da wasu korafe-korafe hukumar DSS da na yan sandan birnin tarayya domin su taimaka wajen gano inda yake.

“Da aka samu bayanai game da shi a ranar Alhamis da ta gabata, ya yi zargin cewa wasu mutane na son kashe shi. Tun daga lokacin wayarsa a kashe take.

“A zaman kotu na ranar Juma’a, alkali ya bukaci Ndume da ya fito da shi a ranar Litinin amma ko sama ko kasa ba a gansa ba, hatta dansa da ya kan zo kotu akai-akai, an neme shi an rasa.

“Hukumar DSS sun ce idan har bata samu izini ba daga kotu, babu yadda za a yi ta tura jami’anta su kama shi.”

An tattaro cewa an je an gudanar da bincike a asibitin da ya fada ma kotu cewar nan yake zuwa.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin ƙasa: Za mu goyi bayan Igbo a 2023 - Sarkin Hausawa

“Mun je asibitin, ba mu gan shi ba domin babu wata alama na kwantar dashi a asibitin a baya-bayan nan,” in ji babbar majiya.

An tattaro cewa an matsa wa Ndume kan ya janye lamuninsa kan Maina.

Wata majiyar ta kara da cewa: “A yanzu Ndume na fuskantar matsin lamba kan ya nemi kotu ta soke lamuninsa tunda ya kasa gano Maina.

“Wasu dattawan Borno ne suka nemi sanatan ya tsaya masa saboda Maina ya fito daga mazabarsa. Wadannan dattawa sun sha kunya a kan yadda lamarin ya koma.”

A wani labari na daban, Sufetan ‘Yan sandan Najeriya na kasa, ya shigar da karar tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, a wani babban kotun tarayya da ke Abuja.

Shugaban ‘yan sandan ya na zargin tsohon gwamnan da laifuffuka uku da su ka hada da sata da kuma amfani da sunan wani wajen yaudarar mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel