Da duminsa: Sabbin mutane 155 sun kamu cutar Coronavirus yau, yayinda ake dab da shiga 60,000

Da duminsa: Sabbin mutane 155 sun kamu cutar Coronavirus yau, yayinda ake dab da shiga 60,000

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 155 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Laraba 7 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 155 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-84

Rivers-31

Kaduna-12

Osun-10

FCT-7

Oyo-6

Ogun-3

Kwara-2

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 59,738, sai kuma mutum 50,403 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1113 suka riga mu gidan gaskiya.

Ga jerin adadin mutanen da suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:

Legas - 19,776

Abuja - 5,765

Filato - 3,498

Oyo - 3,279

Edo - 2,634

Ribas - 2,632

Kaduna - 2,463

Ogun - 1,898

Delta - 1,803

Kano - 1,738

Ondo - 1,638

Enugu - 1,289

Ebonyi - 1,050

Kwara - 1,050

Abia - 898

KARANTA NAN: Dukkan masu rajin yakin neman Biyafara mahaukata ne - Babban Malamin Katolika

Gombe - 894

Katsina - 893

Osun - 874

Borno - 745

Bauchi - 704

Imo - 577

Benuwe - 481

Nasarawa - 468

Bayelsa - 401

Jigawa - 325

Sakkwato - 162

Neja - 293

Akwa Ibom - 293

Adamawa - 248

Kebbi - 93

Zamfara - 79

Anambra - 250

Yobe - 76

Ekiti - 322

Taraba - 106

Kogi - 5,

Cross River - 87

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel