Ganduje zai gina makarantu na musamman a masarautun Kano 5
- A cikin shekarar 2019 gwamnatin Kano ta kirkiri dokar samar da wasu karin masarautu guda hudu a jihar
- Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kirkirar sabbin masarautun zai kawo cigaba cikin gaggawa a sassan jihar
- Kwamishinan ilimi a jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa'id Kiru, ya ce kowacce masarauta za ta samu makaranta ta musamman
Gwamnatin jihar Kano ta sahale gina manyan makarantun haɗaka guda biyar a masarautun jihar daban-daban.
Makarantu zasu fara aiki ne daga zangon karatu na shekarar 2021/2022.
Kwamishinan ilimi na jihar kano Malam Muhammad Sunusi Sa'id Ƙiru,yace kowacce masarauta zata rabauta da makarantar haɗaka guda ɗaya.
A bayanan da jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilmi, Aliyu Yusuf, ya fitar yac e wannan shawarar na daga cikin matsaya da majalisar zartawar jihar ta cimma a taron da ta gudanar ranar Talata.
DUBA WANNAN: Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sabbin makamai na zamani
Rahotanni sun tabbatar da cewa kowacce makarantar haɗaka za ta samar da gurbin ɗalibai 360.
Inda makarantu zasu fara da ajuzuwan Js1, Js2, Js3 da kuma SS1 daga zangon karatu na shekarar 2020/2021.
"Sanusi Ƙiru ya ƙara da cewa da zarar an kammala waɗannan makarantu zai zamana jihar tana da makarantun haɗaka bakwai kenan in aka haɗa da na garin Ƙiru da kuma Kachako.
DUBA WANNAN: Bayan mutuwar mutane 23 a makon jiya; Tankar mai ta sake faduwa a Lokoja
"Makarantun haɗakar za su bawa ɗalibai daga sauran jihohin arewa 18 gurbin karatu" a cewar sa.
Ya ƙara da cewar Daraktoci sune zasu shugabanci makarantu a matsayin shugabannin makarantun inda kuma mataimakan Daraktoci zasu kasance a matsayin mataimakan shugabanni a sashen karatu da kuma gudanarwa don samun ilmi mai inganci da kuma ƙarko.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng