Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Farfesa Isa Dutse

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Farfesa Isa Dutse

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban asibitin koyarwa ta Aminu Kano, Faresa Isa Dutse

- Shugaban kasar ya ce rasuwar Farfesa Isa Dutse babban rashi ne ga fanin likitanci da Najeriya musamman a lokaci irin na yanzu da ake bukatarsa

- Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin ya saka masa da gidan aljanna ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa

Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bakin cikinsa bisa rasuwar Farfesa Abdulahamin Dutse, tsohon shugaban Asibitin Koyarwa Ta Aminu Kano, inda ya ce mutuwarsa "babban rashi ne ga bangaren likitanci."

DUBA WANNAN: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin sakon ta'aziyya da ta fito daga bakin kakakinsa Garba Shehu a ranar Laraba a Abuja.

A cewarsa, rasuwar Farfesa Dutse ya tauye wa Najeriya daya daga cikin manyan likitocin da suka sadaukar da kansu wurin aikinsu.

Ya kara da cewa an rasa marigayin ne a lokacin da kasar ke bukatarsa sosai sannan ya ce za ayi kewarsa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe jami'in kwastam da wasu 9 a Katsina

Ya ce: "Daga abinda abokan aikinsa da dalibansa ke fada a kansa bayan rasuwarsa, Isa Dutse tabbas mutum ne da ya bada gudunmawa sosai a fanin likitanci, Najeriya da al'umma baki daya.

"A matsayinsa na tsohon shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano, marigayi Farfesa Isa Dutse ya bar halaye na gari da zai zama abin koyi da na baya gare shi da abokan aikinsa.

"Ina son yi amfani da wannan daman don mika ta'aziyya ta ga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, gwamnatin jihar Jigawa da Kungiyar Likitoci ta Najeriya bisa rasuwar fitaccen likita.

"Da fatan Allah ya yi masa gafara ya saka masa da aljanna."

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sabunta wa'addin shugaban Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria na tsawon shekaru hudu.

Sakatariyar dindindin na Ma'aikatar Sufuri, Dakta Magdalene Ajani ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwar da ta raba wa manema labarai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel