Bayan mutuwar mutane 23 a makon jiya; Tankar mai ta sake faduwa a Lokoja

Bayan mutuwar mutane 23 a makon jiya; Tankar mai ta sake faduwa a Lokoja

- A makon jiya ne wata tankar dakon man fetur ta fadi a garin Lokoja, jihar Kogi, tare da kashe mutane a kalla 23

- Mako guda bayan faruwar hakan, wata tankar dakon man ta sake faduwa a garin Lokoja a yau, Laraba, 07 ga watan Oktoba

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya dora alhakin faduwar manyan motocin a kan gazawar gwamnatin tarayya na gyara hanyoyinta

Mako guda bayan wata tankar dakon mai makare da fetur ta fadi tare da zama silar ajalin mutane 23, wata tankar ta sake faduwa a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A wannan karon, motar ta fadi ne sakamakon wani hatsari da ya ritsa da ita a yankin Felele da ke cikin birnin Lokoja.

A kalla mutane 23 jaridar Premium Times ta wallafa cewa sun rasa rayukansu sakamakon faduwar tankar dakon mai a ranar 23 ga watan Satumba a Lokoja.

Da ya ke jawabi a kan faruwar lamarin, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya dora laifin a kan sakacin gwamnatin tarayya wajen gyara hanyoyinsu da su ka lalace.

DUBA WANNAN: Rundunar yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami'anta sun ci zarafin mutum

Kazalika, Gwamnan ya ja hankalin ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, a kan a duba halin da hanyar ke ciki.

Bayan faruwar hakan ne kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fitar da sanarwar cewa wata tankar dakon mai makare da fetur ta sake faduwa a Lokoja ranar Laraba.

Bayan mutuwar mutane 23 a makon jiya; Tankar mai ta sake faduwa a Lokoja
Tankar dakon mai ta sake faduwa a Lokoja
Asali: UGC

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin cewa ba a samu asarar rayuka ba sakamakon faduwar tankar a wannan karon.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sabbin makamai

"Gwamnati ta dauki matakan kiyayewa, sannan mu na kira ga jama'a a kan su guji zuwa kwarfar mai a duk lokacin da motar dako ta fadi.

"Mazauna yankin za su iya cigaba da harkokinsu, saboda gwamnati ta tura jami'anta da sauran ma su ruwa da tsaki domin ganin cewa ba a samu wata matsala ba," a cewar sanarwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel