NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi

NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace wajibi ne a kiyaye dokokin kariya daga cutar COVID-19 a taron da za'ayi a majalisar

- Yace za'ayi taron gabatar da kasafin kudaden 2021 a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba kamar yadda aka saba, amma sai anyi nesa-nesa da juna

- Yace a shekarun baya, gwamnoni, ministoci da hadiman Buhari suna raka shi, amma a wannan karon mutane kadan ne zasu samu shiga

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace za'ayi amfani da dokokin kare kai daga cutar COVID-19 a ranar Alhamis idan Buhari zai gabatar da kasafin kudaden 2021.

Yace da yawa daga cikin hadiman Buhari ba za su samu damar shiga majalisar ba. Duk wanda ke sha'awar ganin abubuwan da ke faruwa zai iya dubawa ta yanar gizo.

Duk da a shekarun baya gwamnoni, ministoci, shuwagabannin jam'iyyar APC da kuma hadiman Buhari na gaba-gaba wurin raka shi.

Bayan Lawan ya gama wannan jawabin ne sai sanatan Arewacin Kebbi, Yahaya Abdullahi ya gabatar da batun yadda 'yan majalisar wakilai zasu saurari bayani daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2020 da karfe 11 na safe akan kasafin kudaden 2021.

Shugaban majalisar dattawan yace za'ayi gabatarwar na tsawon awa 1. Kamar yadda yace, shugaban kasa zai yi bayani ne a majalisar wakilai.

"Za'ayi komai yadda aka saba. Amma wannan karon, saboda cutar COVID-19, zamu yi amfani da dokar nesa-nesa da juna a majalisar.

"Wajibi ne kowa yasa takunkumin fuska, kuma zamu yi kokarin kiyaye dokoki saboda za'a taru sosai.

"Don haka gaba daya taron na awa daya kadai za'ayi, tun daga shigowar shugaban kasa majalisar da duk wata gabatar wa, dole ne mu kiyaye dokokin kariya daga cutar COVID-19.

"Sannan wannan karon mutane kadan ne zasu rako shugaban kasa," a cewarsa.

KU KARANTA: An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi
NASS ta hana wasu hadimai da ministocin Buhari rakiyar gabatar da kasafin kudi. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Edo, Rt. Hon. Frank Abumere Okiye da wasu 'yan majalisar jihar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba. Sun bar jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyya mai ci ta PDP.

Bayan Okiye ya sanar da sauya jam'iyyarsa, ya ce an turo masa wasiku 6 na sauya jam'iyya. Sun ce sun sauya jam'iyya ne don su nuna yadda suke biye da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel