Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu

Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu

- Sakataren Masarautar Kano, Alhaji Mahmudu Aminu Bayero, ya rasu

- Allah ya yi wa Bayero rasuwa ne a yau Laraba, 7 ga watan Oktoba

- Za a yi jana’izarsa da karfe 2:00 na rana a Kofar Kudu da ke Masarautar Dabo

Rahoto da muke samu a yanzu ya nuna cewa, Allah ya yi wa Sakataren Masarautar Kano, Alhaji Mahmudu Aminu Bayero, rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

A bisa ga sanarwar da Masarautar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce za a yi jana’izarsa da misalign karfe 2:00 na rana a Kofar Kudu da ke Masarautar Dabo, birnin Kano.

Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu
Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki

A wani labari na daban, mun ji cewa mutum tara ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kano.

Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, a jihar cikin wata sanarwa da ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 9 na safe da ya ritsa da mota da adaidaita sahu a hanyar Kano zuwa Zaria a kauyen Imawa da ke karamar hukumar Kura.

Kwamandan ya ce hatsarin ya ritsa da trela mai lamba KMC158XW, wata karamar mota mai lama AE 884 GZW da adaidaita sahu mara lamba.

Ya ce trelan da motar sun yi karo ne a kokarin su na kaucewa adaidaita sahun da ke taho wa daga ta dayan bangaren titin.

Kwamdan ya ce cikin wadanda suka rasu akwai maza biyu, mata shida da yaro daya sai kuma wadanda suka jikkata su uku suna babban asibitin Kura da ke Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng