Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa yan majalisan wakilan tarayya biyu sun sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Yan majalisan sune David Abel daga jihar Taraba da kuma Ephraim Nwuzi daga jihar Rivers.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya sanar da hakan a zauren majalisa yau Laraba.

A cewar majalisar a jawabin da ta daura a shafinta na Tuwita, "Bayan addu'ar bude taro...Kakaki ya karanta wasikar sauya shekan dan majalisa Ephraim Nwuze daga Rivers da Abel David daga Taraba."

Dukkansu biyun sun bayyana cewa irin namijin kokarin kakakin majalisar ne yasa zasu sauya sheka daga PDP zuwa APC."

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC
Credit: @HouseNGR
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel