Najeriya ta yi dacen shugaba, Buhari ya kawo babban cigaba a bangaren fasaha - Pantami

Najeriya ta yi dacen shugaba, Buhari ya kawo babban cigaba a bangaren fasaha - Pantami

- An shirya wani muhimmin taro domin tattaunawa tare da nuna irin cigaban da Najeriya ta samu a bangaren fasahar zamani

- Cibiyar 'Innovation Hub Africa' ce ta shirya taron mai taken 'Nigeria Innovation Summit 2020' wanda aka yi ranar Talata a Abuja

- Shugaban hukumar NITDA, Mallam Kashifu Inuwa, ne ya wakilci ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, a wurin taron

Ministan sadarwa da gina sabon tsarin tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya yabawa kokarin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A cewar ministan, shugaba Buhari ya taimaka matuka wajen saka Najeriya a sahun gaba a cikin kasashen nahiyar Afrika da duniya da su ke taka rawar gani a bangaren fasahar zamani.

Ministan ya jinjinawa shugabancin Buhari a kan kokarin dora Najeriya a kan tafarkin cigaba duk da tsaikon da tattalin arziki ya samu saboda ballewar annobar korona.

Pantami ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar NITDA, Mallam Kashifu Inuwa, wanda ya wakilce shi a wurin wani taro da aka shirya a Abuja.

Wata cibiya ce mai suna 'Innovation Hub Africa' ta shirya taron mai taken 'Nigeria Innovation Summit 2020' wanda aka yi ranar Talata a Abuja.

"Mu, a Najeriya, mun yi dace da shugabanci a irin wannan lokaci. Gwamnatin kasa, a karkashin jagorancin shugaba Buhari, ta saka tubalin cigaban Najeriya tun kafin bullar annobar korona," a cewar wani bangare na jawabin Pantami da Inuwa ya karanta.

Yayin taron, yara ma su tasowa sun nuna irin basirarsu a gasar kera na'urori ma su sarrafa kansu da aka gudanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel