Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno

Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno

- 'Yan Boko Haram sun kashe daya daga cikin jaruman jami'an JTF, Babagana Idi a jihar Borno

- Babagana Idi da wasu jami'an JTF sun fuskanci 'yan Boko Haram a maboyarsu ta karamar hukumar Magumeri

- Bayan musayar wuta, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 2, sun kuma kama 1 da ran sa

'Yan Boko Haram sun kashe daya daga cikin jami'in JTF, Babagana Idi, yayin da suke musayar wuta da su a karamar hukumar Magumeri dake jihar Borno.

Al'amarin ya faru ne da daren Litinin, 5 ga watan Oktoba, inda suka je maboyar 'yan Boko Haram dake Megumeri.

Wani Abba Audu, yayi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, ya bayyana Babagana a matsayin jarumi.

Yayin da suka isa maboyar 'yan Boko Haram, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 2, sun kuma kama 1 da ransa.

"Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un, wani sadauki ya tafi, anyi mummunar asara," A yadda ya wallafa.

"A jiya ne jami'an JTF ta Benisheikh Command suka tunkari maboyar Boko Haram a dajin karamar hukumar Magumeri, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 2, sun kuma kama 1.

"Sai dai sun kashe jarumi kuma gwarzo Babagana Idi, yayin da suke musayar wuta da 'yan Boko Haram. Muna fatan Allah ya jikan Babagana Idi, ya kuma gafarta masa ya sa aljanna ta zama makomar sa," yace.

Anyi jana'izar Idi da karfe 10 na dare a Benisheikh, a karamar hukumar Kaga a jihar Borno.

KU KARANTA: Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo

Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno
Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno. Hoto daga Mahmud Pantami
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci

A wani labari na daban, Farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar da wani jawabi a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, inda yace babban abinda ya dace a kalla idan za'a dora mutum a mukamin gwamnati shine kwazonsa, ba wani matsayin da ya taba rikewa ba a gwamnati.

Osinbajo ya fadi hakane a wani taro da NLI suka shirya, inda yace hakan zai taimaka wurin bunkasa tattalin arzikin kasa kamar yadda jaridar The Cable suka ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: