Za mu fara binciken karkatar da kudin ciyarwa N2.6bn - FG

Za mu fara binciken karkatar da kudin ciyarwa N2.6bn - FG

- A makon jiya ne hukumar ICPC ta sanar da cewa an karkatar da kudin ciyar da dalibai N2.bn da gwamnati ta ware

- Ministar walwala da bayar da tallafi, Sadiya Umar Farouk, ta sanar da cewa FG ta kashe makudan daruruwan miliyoyi wajen ciyar da dalibai lokacin korona

- 'Yan Najeriya da dama sun bayyana bacin ransu dangane da ikirarin ministar na cewa an ciyar da dalibai lokacin dokar kulle saboda annobar korona

Gwamnatin tarayya (FG) ta bayar da umarnin fara cikakken bincike dangane da karkatar da N2.6bn da aka ware domin ciyar da dalibai a lokacin annobar korona.

Ministan ilimi na kasa, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata.

Hukumar ICPC ce ta kwarmata cewa an waske da N2.67bn da aka tura makarantun hadaka guda 104 domin ciyar da dalibai lokacin da aka saka dokar kulle.

A cikin wani jawabi da Ben Going, jami'in hulda da jama'a a ma'aikatan ilimi, ya fitar, ma'aikatar ta yi karin bayani.

A cewar sanarwar, ma'aikatar ilimi ta na tura kudaden ciyarwa zuwa asusun shugannin makarantu domin sayen kayen abinci a wurin 'yan kasuwa.

Ma'aikatar ta ce ta na yin hakan ne domin saukaka al'amura a makarantu 104 da nauyinsu ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya.

Shugabannin makaratun sun bayyana cewa sun samu tangarda wajen biyan kananan manoma saboda wasu matsaloli a tsarin tura kudi na bankuna.

Kazalika, sun yi ikirarin cewa sun yi amfani da wani bangare na kudaden wajen biyan basukan da 'yan kwangila ke bin makarantunsu tun kafin bullar annobar korona.

"Binciken zai duba gaskiyar ikirarin da shugabannin makaratun domin tabbatar da cewa ba a karkatar da kudaden zuwa asusun wasu mutane ba.

"Minista ya bayar da umarnin hada kai da hukumar ICPC domin gano gaskiya tare da warware matsalar da ake samu wajen biyan 'yan kwangila daga asusun gwamnati," a cewar jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel